Arinola Olasumbo Sanya
Arinola Olasumbo Sanya[1] (an haife shi a shekara ta 1953) farfesa ne a fannin ilimin physiotherapy a Jami'ar Ibadan kuma tsohuwar kwamishiniyar lafiya a jihar Oyo, Najeriya. An naɗa Arinola farfesa a shekara ta 2000, inda ta zama farfesa mace ta farko a fannin ilimin physiotherapy a Afirka, kuma ta zama farfesa ta biyu a fannin ilimin physiotherapy a Najeriya. Tana cikin Fitattun ’yan asalin Jihar Oyo.[2]
Arinola Olasumbo Sanya | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1953 (70/71 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ibadan |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Malami da university teacher (en) |
Employers | Jami'ar Ibadan |
Arinola ita ce Mataimakiyar Shugaban Jami'ar Ibadan na yanzu.[3] Arinola ta halarci makarantar Salvation Army Primary School da ke Surulere Legas.
Bayan ta kammala, ta halarci Kwalejin Queens, Yaba, Legas inda aka mai da ita Head Girl. Ta sami horo a matsayin Likitar Jiki a Jami'ar Ibadan, Cibiyar Horar da physiotherapy ta Firimiya ta Kudu da Sahara. Ta shiga Sashen Nazarin physiotherapy a Jami'ar Ibadan a matsayin mataimakiyar malami a shekarar 1978 inda ta ci gaba da zama Farfesa. Arinola mai ba da shawara ne ga fannin Physiotherapist a Asibitin Kwalejin Jami'ar (UCH), Ibadan.
Ta zauna a cikin kwamitocin matakin gudanarwa da yawa a Jami'ar Ibadan kamar kwamitin nadi da cigaba.[4]
Sabis na jama'a
gyara sasheAn nada ta kwamishiniyar lafiya a jihar Oyo (Nigeria) a shekarar 2005.[5]
Iyali
gyara sasheFarfesa Sanya ta auri Dr. Yemi Sanya, masanin harhaɗa magunguna kuma hamshakin attajiri a birnin Lagos na Najeriya. Suna da yara hudu.[6]
Wallafe-wallafe
gyara sashe- Physical treatment of Buruli (Mycobacterial) ulceration in Nigeria: a case study report[7]
- Constraint - Induced Movement Therapy: Determinants and Correlates of Duration of Adherence to Restraint use Among Stroke Survivors with Hemiparesis[Ana bukatan hujja]
- Risk factors for low back pain among hospital workers in Ibadan, Oyo State, Nigeria[8]
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "CITATION OF PROFESSOR ARINOLA OLASUMBO SANYA | UNIVERSITY OF IBADAN". ui.edu.ng (in Turanci). Retrieved 2017-12-22.
- ↑ "UI appoints new DVC, registrar — the Punch - Nigeria's Most Widely Read Newspaper". Archived from the original on 2012-04-28. Retrieved 2012-05-12.
- ↑ "CITATION OF PROFESSOR ARINOLA OLASUMBO SANYA | UNIVERSITY OF IBADAN". www.ui.edu.ng. Archived from the original on 2021-05-20. Retrieved 2021-05-20.
- ↑ "CITATION OF PROFESSOR ARINOLA OLASUMBO SANYA | UNIVERSITY OF IBADAN". www.ui.edu.ng. Archived from the original on 2021-05-20. Retrieved 2021-05-20.
- ↑ "Arinola Olasumbo Sanya". www.wikidata.org (in Turanci). Retrieved 2021-05-20.
- ↑ "Nigeria Physiotherapy Network-Arinola O. Sanya". www.nigeriaphysio.net. Retrieved 2022-08-10.
- ↑ Sanya, Arinola Olasumbo (1986-01-01). "Physical treatment of Buruli (Mycobacterial) ulceration in Nigeria: a case study report". Physiotherapy Practice. 2 (3): 138–141. doi:10.3109/09593988609022434. ISSN 0266-6154.
- ↑ Sanya, A. O.; Omokhodion, F. O.; Ogwumike, O. O. (2005-10-01). "Risk factors for low back pain among hospital workers in Ibadan, Oyo State, Nigeria". Journal of the Nigeria Society of Physiotherapy (in English). 15 (2): 31–35.CS1 maint: unrecognized language (link)