Angela Okolo, farfesa ce ta Najeriya a fannin ilimin yara da lafiyar yara, likitar jarirai a sashen kula da lafiyar yara, Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Asaba kuma Shugabar kungiyar likitocin jarirai ta Najeriya (NISONM).[1]

Angela Okolo
Rayuwa
Karatu
Makaranta Lovanium University (en) Fassara
(1 Satumba 1965 - 1 ga Yuli, 1971) Doctor of Medicine (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Malami
Employers University of Benin Teaching Hospital  (1 ga Yuli, 1972 -  1 ga Yuli, 1977)
Jami'ar jahar Benin  (14 Satumba 1977 -  30 ga Afirilu, 2016)

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

Ta fito daga jihar Delta a Najeriya. Ta fara balaguron neman ilimi a St. Theresa's Primary Catholic School Jos, sannan ta wuce St. Louis College Kano domin yin karatun sakandare. Daga baya ta ci gaba da karatun likitanci a Jami'ar Lovanium, Kinshasa, DRC Afirka ta Tsakiya daga shekarun 1965 zuwa 1971 inda ta kuma sami digiri na asali na ''Docteur en Medicine''.[2] Jim kaɗan bayan ta fara horon karatun digiri na biyu a matsayin likita a fannin lafiyar yara a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Benin a jihar Edo, Najeriya tsakanin shekarun 1972 zuwa 1977. A lokacin wannan karatun, ta sami memba na Kwalejin Royal na Likitoci da Likita na Glasgow a shekarar 1977[3] sannan ta zama fellow na Royal College of Physicians and Surgeons na Glasgow a shekarar 1987 kuma ta zama fellow na Royal College of Pediatrics and Child Lafiya (Birtaniya) a cikin shekarar 1997.[4] Daga baya aka naɗa ta a matsayin malama a jami’ar Benin inda daga baya ta zama farfesa daga shekarun (1977 zuwa 2016).[2]


Ita ce mai ba da shawara ga fannin likitanci na yara kuma farfesa a fannin ilimin yara wacce ta yi karatun Neonatology a karkashin Jami'ar Koyarwa ta Jami'ar Benin (1972-har zuwa yau). A cikin wannan ma'aikata, tana ba da gudummawa a cikin koyarwa da bincike kan ilimin haihuwa da lafiyar mahaifa. Tana karantarwa a cibiyoyi daban-daban daya daga cikinsu ita ce Jami'ar Jihar Delta.[5]

Ita ma likitan Neonatologist ce a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya Asaba. Ta yi aiki tare da kungiyoyi daban-daban kamar WHO, UNICEF,[6] da ECOWAS a karkashin kungiyar lafiya ta Afirka ta Yamma don inganta lafiyar yara. Ta shiga ayyuka daban-daban kuma ta yi wallafe-wallafe da yawa.

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Okolo na da aure da ‘ya’ya biyu.[4] Ita 'yar asalin kasar Ingila ce, kuma tana iya yaren Ibo, Hausa, Yoruba, da Faransanci.[4] Ita Kirista ce ta bangaskiyar Katolika, memba ce ta Kungiyar Matan Katolika da Uwargidan Knights na Saint Mulumba (LSM).[4]

Membobin kungiya

gyara sashe
  • Sickle cell society of Nigeria (SCSN)[4]
  • American Academy of Pediatrics (AAP)[7]
  • European society for pediatric endocrinology (ESPE)[8]
  • Nigerian society of neonatal medicine(NISOMN)[8]
  • Union of National African pediatric societies and association (UNAPSA)[9]
  • International pediatric association (IPA)[10]

Bincike da wallafe-wallafe

gyara sashe
  • The management of severe tetanus using magnesium sulfate- the experience ina tertiary health institution in Southern Nigeria.[11]
  • Postnatal Magnesium Sulfate in Asphyxiated Newborns in Benin City Nigeria: Effect on Mortality[12]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Edo First Lady Rolls Out Plan On Neonatal, Maternal health Awareness". THISDAYLIVE (in Turanci). 2017-10-27. Retrieved 2020-04-19.
  2. 2.0 2.1 "Anene Okolo (0000-0003-1527-1164)". orcid.org.
  3. "Death of less than one-month old babies accounts for 40% infant mortality — Society". SundiataPost (in Turanci). 2014-06-26. Retrieved 2020-04-19.
  4. 4.0 4.1 4.2 4.3 4.4 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named auto1
  5. "Extreme Corruption And Abuse Of Office By Prof. Joseph Otubu: A Call To Put An Urgent Halt To This Evil". Sahara Reporters. November 16, 2012.
  6. [1][dead link]
  7. "Prof. Angela Anene Okolo | International Journal of TROPICAL DISEASE & Health". www.journalijtdh.com.
  8. 8.0 8.1 Leo, Ruby (July 1, 2014). "Neo-natal society moves to ensure survival of infants". Daily Trust.[permanent dead link]
  9. "About us". UNAPSA.[permanent dead link]
  10. "ABOUT US - unapsa". sites.google.com.
  11. "MANAGEMENT OF SEVERE TETANUS USING MAGNESIUM SULFATE – THE EXPERIENCE IN A TERTIARY HEALTH INSTITUTION IN SOUTHERN NIGERIA". www.researchgate.net. 2019. Retrieved 2020-06-14.
  12. "Postnatal Magnesium Sulfate in Asphyxiated Newborns in Benin City Nigeria: Effect on Mortality". www.researchgate.net. 2019. Retrieved 2020-06-14.