Amarachi Grace Okoronkwo (an haife ta a ranar 12 ga watan Disamba, shekara ta alif 1992), [1] ita ce ‘yar wasankwallon kafa ta Najeriya wadda yanzu take taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa Amazons a gasar Firimiya ta Mata ta Najeriya da kuma kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya. Ta taba buga wa Koka Kola F10 a Naisten Liiga ta Finland ta dauki gasar Afirikan woman champion a shekarar 2010.

Amarachi Okoronkwo
Rayuwa
Haihuwa Owerri, 12 Disamba 1992 (31 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Harshen Ibo
Karatu
Harsuna Turanci
Harshen Ibo
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya-
Nasarawa Amazons (en) Fassara-
Kokkola Futis 10 (en) Fassara2012-2013467
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Tsayi 1.63 m

Ayyuka gyara sashe

Klub din gyara sashe

Saboda rawar da ta taka wajen jagorantar Nasarawa Amazons don lashe gasar Firimiyar Mata ta Najeriya ta shekarar 2017, Okoronkwo na daga cikin ‘yan wasa hudu da aka zaba a matsayin mafi kyaun 'yar wasan NWPL na shekara, amma ta rasa kyautar ga Rasheedat Ajibade. A watan Mayu na shekarar 2018, an zabe ta a matsayin wadda ta fi kowa a gasar Firimiya ta Mata ta Najeriya a shekarar 2017, a gasar Nigeria "Pitch Awards" , amma ta sha kashi a hannun Ajibade.

Na duniya gyara sashe

Okoronkwo ta wakilci Najeriya a Gasar Matan Afirka ta 2010. An kira ta ne don wasan sada zumunci da Jamus a matsayin shirye-shiryen halartar Najeriya a Gasar Kofin Duniya ta Mata ta FIFA .

A cikin shekarar 2018, Okoronkwo ta buga wa Najeriya gasar cin kofin WAFU ta mata ta 2018, inda ta lashe tagulla ga kungiyar. Ta kuma kasance cikin tawagar kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya a gasar cin kofin kasashen Afirka ta mata ta 2018, kuma ta lashe gasar tare da kungiyar. [2]

Daraja gyara sashe

  • Gasar Mata ta Afirka a 2010 - wadanda suka yi nasara.
  • Kofin mata na WAFU 2018 - matsayi na uku.
  • 2017 Nigeria Premier League - masu nasara.
  • Gasar Kofin Afirka ta Mata ta Afirka - masu nasara.

Manazarta gyara sashe

Hanyoyin haɗin waje gyara sashe

  • Amarachi Okoronkwo – FIFA competition record
  • Amarachi Okoronkwo at Soccerway