Amarachi Okafor (an haife ta a shekara ta alif ɗari tara da saba'in da bakwai 1977) yar zane-zanen ce a Najeriya, kuma wacce take ayyukan ta akan al'adu, addini, tarihi, alaƙar jinsi, jima'i na ɗan adam, da kuma batutuwan da suka shafi duniya, kamar yaɗuwar cutar Ebola a Afirka. [1]

Amarachi Okafor
Rayuwa
Haihuwa Umuahia, 1977 (46/47 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Harshen Ibo
Karatu
Makaranta Jami'ar Najeriya, Nsukka
Harsuna Turanci
Harshen Ibo
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Masu kirkira


Rayuwar farko da ilimi gyara sashe

Okafor haifaffiyar garin Umuahia ce,[2] A shekara ta dubu biyu da biyu 2002 ta halarci kwasa-kwasan koyar da fasaha a Jami'ar Nijeriya kuma a shekarar dubu biyu da bakwai 2007, a wannan Jami’ar, ta yi digirin ta na biyu a bangaren sassaka abubuwa da kuma aikin koyo. [3]

Aikin ta gyara sashe

Okafor memba ce a El Anatsui ta Atelier a cikin shekarar 1990s.[4]

Okafor tana aikin zane-zane da sassaka. Ita ce mai kula da NGA (National Gallery of Art) a Abuja, tsakanin shekarar 2008 da kuma 2014.[5] A cikin 2007 ta ci nasarar zama a cikin unesco-Aschberg ƙungiya na masu zane-zane, da kuma Commonwealth Foundation Commonwealth Connections a cikin 2010. A shekarar 2014, ta kasance a lis din karshe a gasar kere kere ta kasa ta 2014, [6] kuma ta lashe kyautar Juror a waccan shekarar.[7][8]

Ta baje kolin ta a 2015 Jogja Biennal[9]

Manazarta gyara sashe

  1. Nnadozie, Uche (27 November 2014). "From Office to Studio,NGA Artists Preach Peace". Vanguard. Retrieved 8 February 2016.
  2. http://www.imagomundiart.com/artworks/amarachi-okafor-duo-totem-emmissaries/
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2017-12-14. Retrieved 2020-11-14.
  4. https://doi.org/10.4000%2Fetudesafricaines.18555
  5. https://en.m.wikipedia.org/wiki/Amarachi_Okafor#cite_note-6
  6. http://www.premiumtimesng.com/news/167119-12-finalists-emerge-for-national-art-competition.html
  7. http://www.premiumtimesng.com/news/167119-12-finalists-emerge-for-national-art-competition.html
  8. https://web.archive.org/web/20150320080802/http://www.thisdaylive.com/articles/an-evening-of-surprising-interventions/196051/
  9. https://web.archive.org/web/20150320080802/http://www.thisdaylive.com/articles/an-evening-of-surprising-interventions/196051/

Hanyoyin haɗin waje gyara sashe

  • Official website