Abdukareem Adebisi Bamdele Akande ("Bisi Akande"; an haife shi a ranar goma sha shida 16 ga watan Janairu shekara ta alif dubu daya da dari tara da talatin da tara 1939) shi ne gwamnan jihar Osun, Nijeriya daga shekara ta (shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da tara 1999 zuwa shekarar alif dubu biyu da ukku 2003) a matsayin memba na jam'iyyar Alliance for Democracy (AD), kuma shi ne Shugaban riko na farko na All Progressives Congress.

Adebisi Akande
Gwamnan Jihar Osun

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2003
Theophilus Bamigboye (en) Fassara - Olagunsoye Oyinlola
Rayuwa
Haihuwa Ila Orangun, 23 ga Janairu, 1939 (85 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Yaren Yarbawa
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress
Alliance for Democracy (en) Fassara

Farkon rayuwa

gyara sashe

Cif Adebisi Akande an haife shi a Ila Orangun a ranar goma sha shida 16 ga watan Janairun shekara ta alif dubu daya da dari tara da talatin da tara 1939 a yankin da ake kira Osun Central Senatorial a yanzu. An zabe shi ne a kan dandalin Unity Party of Nigeria (UPN). An bayyana Akande a matsayin dan wa ga Cif Bola Ige.

Aikin gwamna

gyara sashe

An zaɓi Akande a matsayin gwamnan jihar Osun a watan Afrilun shekara ta alif dubu daya da dari tara da casa'in da tara (1999) yana takarar jam’iyyar Alliance for Democracy (AD), wacce a baya-bayan nan ta kafa kungiyar siyasa ta kungiyar yarbawa ta Afenifere. Ya gaji Kanar Theophilus Bamigboye, wanda aka nada a matsayin mai kula da mulkin soja na jihar a watan Agustan shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da takwas (1998) wanda kuma ya mika mulki a ranar ashirin da tara 29 ga watan Mayu a shekara ta alif dubu daya da dari tara da casa'in da tara (1999) A ranar talatin da daya 31 ga watan Mayu a shekara ta alif dubu daya da dari tara da casa'in da tara (1999) Akande ya kaddamar da majalisa ta biyu a jihar Osun.

Akande ya sake tsayawa takara a shekarar alif dubu biyu da ukku (2003) amma Prince Olagunsoye Oyinlola na jam’iyyar People's Democratic Party (PDP) ya kayar da shi.

Manazarta

gyara sashe

https://web.archive.org/web/20110724235004/http://www.alliancefordemocracyusa.org/prelease.htm