Alhassan Bako Zaku
Alhassan Bako Zaku (an haife shi a ranar 18 ga watan Janairun a shekarar ta alif ɗari biyar da hamsin da ɗaya (1951) ya zama Ministan Kimiyya da Fasaha na Najeriya a cikin watan Disambar shekara ta 2007.[1] Ya bar mulki a cikin watan Maris ɗin shekarar 2010 lokacin da muƙaddashin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya rusa majalisar ministocinsa.[2]
Alhassan Bako Zaku | |||
---|---|---|---|
17 Disamba 2008 - 17 ga Maris, 2010 ← Grace Ekpiwhre - Muhammed K. Abubakar → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Ibi (Nijeriya), 18 ga Janairu, 1951 (73 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | civil servant (en) |
Fage
gyara sasheAn haifi Alhassan Bako Zaku a garin Dampar dake ƙaramar hukumar Ibi dake jihar Taraba. Ya halarci Makaratar Kwaleji Barewa,dake Garin Zaria a shekarar ta 1965 izuwa 1971. Sannan ya cigaba da karatu a Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria acikin shekarar ta 1972 zuwa shekarar 1979. inda ya samu digiri na B.sc (Education) a 1976, sannan digiri na biyu wato M.Ed a shekara ta 1979. A shekarar 1978, ya shiga Kwalejin Ilimi ta Jalingo a matsayin malami. Ya tafi Jami'ar Hull, Ingila a cikin shekarar 1981, inda ya sami digiri na uku a shekarar 1983. Kimiyya da Ilimin Fasaha. Ya koma kwalejin ilimi ta Jalingo kuma an yi shi a shekarar 1986.[3]
Dokta Bako Zaku ya taimaka wajen kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Adamawa a tsakanin shekarar 1991 zuwa shekarar 1993, kuma shi ne shugabanta na farko. Ya koma Jihar Taraba inda ya kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar a Jalingo a shekarar alif 1993, inda ya zama shugaban gwamnati. Ya yi aiki a National Open University of Nigeria a matsayin Manajan Cibiyar Yola tsakanin shekarar 2001 zuwa 2004, sannan ya koma Kwalejin Ilimi ta Jalingo a matsayin Babban Malami daga shekarar 2004 zuwa 2005. Daga nan ya koma Taraba State Polytechnic, Wukari a matsayin shugaba daga 2005 zuwa Mayun 2007.[3]
Sana'ar siyasa
gyara sasheGwamna Danbaba Danfulani Suntai ya naɗa Alhassan Bako Zaku Sakataren Gwamnatin Jihar Taraba a cikin watan Mayun shekarar 2007, kuma an naɗa shi Ƙaramin Ministan Kimiyya da Fasaha a cikin watan Oktoban shekarar 2007.[3] Bako Zaku ya zama Ministan Kimiyya da Fasaha na Najeriya a watan Disambar shekarar 2008. bayan da ya yi wa gwamnatin Shugaba Umaru Ƴar'aduwa garambawul.[1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 Akin Jimoh, Abiose Adelaja And Christina Scott (2 January 2009). "Country Finally Gets New Health Ministers". SciDev.Net (London
- ↑ https://allafrica.com/stories/201003171041.html
- ↑ 3.0 3.1 3.2 https://web.archive.org/web/20110703235149/http://www.fmst.gov.ng/minister_of_state_profile.php