Alfred Rewane

Ɗan kasuwa a Najeriya

Alfred Rewane, (Agusta 24, 1916 - Oktoba 6, 1995) [1] ɗan kasuwan ne ɗan Najeriya. An kashe shi a ranar 6 ga watan Oktoba, 1995 a gidansa da ke Ikeja, Legas.[2] Ya kasance mai kula da kuɗin NADECO kuma makusanci ne ga Obafemi Awolowo.[3]

Alfred Rewane
Rayuwa
Haihuwa 24 ga Augusta, 1916
ƙasa Najeriya
Mutuwa 6 Oktoba 1995
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa

Tarihin rayuwa gyara sashe

Cikakken sunan Rewane lokacin haihuwa shine Ogbeyiwa Erewarone, an haife shi a Warri ga dangin Jemide Erewarone. Mahaifinsa ɗan kasuwa ne wanda ke zaune a Agbor, lokacin da mahaifinsa baya Warri, Rewane ya zauna tare da kawunsa, a lokacin kuma shi ne ya raɗa ma Rewane suna na farko; Alfred.[4]

Karatu gyara sashe

Ya yi karatu a African School sannan ya yi makarantar gwamnati duk a Warri. Kodayake an shigar da shi Makarantar Grammar Dennis Memorial don karatun sakandare, Rewane bai ci gaba da karatunsa ba.

Aiki gyara sashe

Ya fara aikinsa a matsayin mai horar da manaja tare da UAC kuma ya zama mai kula da bakin teku, Legas Customs Wharf na kamfanin. A cikin 1940s ya bar kamfanin UAC, inda ya mayar da hankali kan shigo da kayayyaki, musamman ƙashin saniya da baƙin barkono, sannan a cikin 1950s, ya kuma shiga kasuwancin harakar katako kuma ya mallaki gidan Rex a Yaba, Legas inda Bobby Benson ya kasance mawaƙi na yau da kullun. A lokacin kafin samun yancin kai a Najeriya, Rewane na da alaƙa da Action Group,[5] ya zama shugaban Kamfanin Raya Yammacin Najeriya wanda ƙungiyar Action Group ke jagorantar gwamnatin yankin.

A cikin shekarun 70s, Rewane ya haɓaka jerin kasuwanci a haɗin gwiwar Sapele tare da Ƙungiyar Seaboard na Amurka. Kamfanonin sun haɗa da masana'antar fulawa ta Life Flour mills, West African Shrimps and Top Feeds.

A shekarun 1990, gidan Rewane a Legas ya kasance wurin taron siyasa wanda ya kai ga kafa NADECO.[6] An san shi a matsayin babban mai kula da kuɗi a ƙungiyar da ke nuna adawa da gwamnatin soja ta Sani Abacha. Rundunar ƴan sandan Najeriya ta kama mutane 7 da ake zargin suna da hannu a kisan sa amma 5 daga cikin waɗanda ake zargin sun mutu a lokacin da ake tsare da su, sauran biyun kuma an sake su ne bisa wasu ƙwararan hujjoji daga masu gabatar da ƙara.

Manazarta gyara sashe

  1. Between Obafemi Awolowo and Alfred Rewane
  2. "Assassination of Pa Rewane: When will Justice be done? - Vanguard News". Vanguard News (in Turanci). 2009-10-17. Retrieved 2018-06-11.
  3. Famoroti, Francis (October 6, 2014). "Remembering Rewane, NADECO chieftain". National Mirror. Archived from the original on February 10, 2015.CS1 maint: unfit url (link)
  4. Nigerian Political Parties: Power in an Emergent African Nation. African World Press. 2004. ISBN 1592212093.
  5. Yorùbá Elites and Ethnic Politics in Nigeria. Cambridge University Press. 2014. ISBN 9781107054226.