Laftanar Janar Akwasi Amankwaa Afrifa (an haife shi a 24 Afrilun shekarata 1936 - ya rasu a 26 Yunin shekarar 1979) soja ne na Ghana, manomi, basaraken gargajiya, marubuci kuma ɗan siyasa . Ya kasance shugaban kasar Ghana na mulkin soja a shekarar 1969. Daga nan ya ci gaba a matsayin manomi kuma ɗan gwagwarmayar siyasa. An kuma zabe shi dan majalisa a 1979, amma an kashe shi kafin ya hau kujerarsa. An kashe shi tare da wasu tsoffin shugabannin kasa biyu, Janar Kutu Acheampong da Janar Fred Akuffo, da wasu Janar-Janar biyar (Utuka, Felli, Boakye, Robert Kotei da Amedume), a watan Yunin shekarar 1979.

Akwasi Afrifa
Shugaban kasar Ghana

2 ga Afirilu, 1969 - 7 ga Augusta, 1970
Joseph Arthur Ankrah (en) Fassara - Nii Amaa Ollennu
Minister for Defence (en) Fassara

1968 - 1969
Minister for Finance and Economic Planning (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Mampong (en) Fassara, 24 ga Afirilu, 1936
ƙasa Ghana
Mutuwa Accra, 26 ga Yuni, 1979
Yanayin mutuwa  (gunshot wound (en) Fassara)
Karatu
Makaranta Royal Military Academy Sandhurst (en) Fassara
Adisadel College (en) Fassara
Mons Officer Cadet School (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da soja
Digiri lieutenant general (en) Fassara
Soja
Imani
Addini Presbyterianism (en) Fassara
Jam'iyar siyasa United National Convention
AkwasiAfrifa.png
Lt.Gen. Akwasi Afrifa

Ilimi da Horon Aikin Soja

gyara sashe

Bayan karatunsa na sakandare a kwalejin Adisadel, ya shiga aikin sojan Ghana a shekarar 1957 kuma aka tura shi zuwa Makarantar Horar da Jami'ai na Musamman. Daga nan ne ya halarci Makarantar ' Mons Officer Cadet School', Aldershot, Ingila a 1958. Sannan ya kammala karatun jami'a a Royal Military Academy, Sandhurst, England . A cikin shekarar 1961, ya kasance a Makarantar Sojan Ruwa, Hythe, United Kingdom .

Harkar Siyasa

gyara sashe

Afrifa ɗa ne ga Opanin Kwaku Amankwa da Ama Serwaa Amaniampong, dukkansu daga Krobo, kusa da Mampong, a Yankin Ashanti. A lokacin da aka kashe shi, ya auri Christine Afrifa, wacce ta haifa masa yara tara. Na farko Ama Serwa Afrifa, bakwai tare da Christine Afrifa; Baffour Afrifa, Baffour Anokye Afrifa, Maame Drowaa Afrifa, Serwaa Amaniampong Afrifa, Ayowa Afrifa, Sophia Afrifa da Akosua Afrifa. An haifi ɗansa na ƙarshe Henry Afrifa bayan mutuwarsa.

Littattafai

gyara sashe
  •  



Manazarta

gyara sashe
  1. ^ a b c d
  2. ^ a b c
  3. ^ a b
  4. ^
  5. ^ a b c d
  6. ^
  7. ^
  8. ^ a b
  9. ^
  10. ^
  11. ^
  12. ^
  13. ^
  14. ^
  15. ^
  16. ^
  17. ^
  18. ^
  19. ^
  20. ^ a b