Akpor Pius Ewherido

Dan siyasar Najeriya (1963-2013)

(4 Mayu 1963 – 30 Yuni 2013) ɗan siyasan Najeriya ne. An zabe shi Sanata mai wakiltar Delta ta tsakiya a zabukan kasa na watan Afrilun 2011, inda ya yi takara a jam'iyyar Democratic People's Party (DPP).[1]

Akpor Pius Ewherido
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015
Adego Erhiawarie Eferakeya (en) Fassara - Ovie Omo-Agege
District: Delta Central
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015
District: Delta Central
Rayuwa
Haihuwa Ughelli, 4 ga Afirilu, 1963
ƙasa Najeriya
Mutuwa 30 ga Yuni, 2013
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (Bugun jini)
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

farkon rayuwa gyara sashe

An haife shi a Ughelli, Ewherido Urhobo ta asali. Ya halarci Kwalejin Notre Dame, Ozoro da Kwalejin Urhobo, Effurun, Ya wuce Jami'ar Ife inda ya karanta Falsafa. Bayan yayi Bautar kasa, Ewherido ya zama dan kasuwa a Warri . Ya kuma karanci fannin shari'a a Jami'ar Benin, daga baya kuma ya zama cikakken lauya.

Siyasa gyara sashe

Ewherido ya shiga jam'iyyar United Nigerian Congress Party (UNCP) a lokacin jamhuriya ta uku ta Najeriya . Bayan da Sani Abacha ya soke mulkin dimokradiyya ya bar harkar siyasa ya koma kasuwanci. A shekarar 1998 ya koma jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) sannan kuma a watan Afrilu 1999 aka zabe shi a matsayin wakilin mazabar Ughelli ta kudu a majalisar dokokin jihar Delta. An nada shi mataimakin kakakin majalisar a wancan lokacin da aka yi taro a watan Yuni 1999. Daga 15 ga Mayu 2000 har zuwa 20 Maris 2001 ya kasance shugaban Majalisar. An sake zaben Ewherido a cikin Afrilu 2003, kuma ya kasance Mataimakin Shugaban Majalisar daga Mayu 2003 har zuwa Mayu 2007. A zaben fidda gwani na PDP na 2006 ya shiga jerin yan takarar gwamnan jihar Delta a zaben da ka gudanar a watan Afrilu 2007, amma bai yi nasara ba a zaben fidda gwani.

Ewherido ya fita daga jam’iyyar PDP ne saboda ya yi takarar kujerar Sanatan ta Delta ta tsakiya a jam’iyyar DPP. A zaben fidda gwani na jam'iyyar DPP, an zabe shi a matsayin dan takara da kuri'u 125, abokin hamayyarsa ya samu kuri'u 108. A zaben watan Afrilun 2011, ya samu kuri’u 102,313, inda Amori Ighoyota na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 85,365.

Mutuwa gyara sashe

Ewherido ya mutune a ranar 30 June 2013.

manazarta gyara sashe

Template:Nigerian Senators of the 7th National Assembly