Ahmed Muhammad Maccido

Dan siyasar Najeriya

Ahmed Muhammad Maccido (an haife shi ne a ranar 1 ga watan Afrilu na shekarar 1964) an zaɓe shi Sanata mai wakiltar mazaɓar Sokoto ta Arewa a jihar Sokoto, Najeriya, ya kuma karɓi mulki ne a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007. Ɗan jam'iyyar PDP ne.[1]

Ahmed Muhammad Maccido
mutum
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Suna Ahmed
Shekarun haihuwa 1 ga Afirilu, 1964
Wurin haihuwa jihar Sokoto
Harsuna Turanci da Pidgin na Najeriya
Sana'a ɗan siyasa
Muƙamin da ya riƙe mamba a majalisar dattijai ta Najeriya da mamba a majalisar dattijai ta Najeriya
Ɗan bangaren siyasa Peoples Democratic Party

Maccido ɗa ne ga marigayi Sultan Muhammadu Maccido.[2] Kafin a zaɓe shi a majalisar dattawa, Maccido ya kasance kwamishinan noma a jihar Sokoto. Bayan kuma ya hau kan kujerarsa a Majalisar Dattawa, sai aka naɗa shi kwamitoci a kan Sojoji, Sufurin Ruwa, Harkokin Majalissar Tarayya, Gidaje, Halin Tarayya & Harkokin Gwamnati da Banki, Inshora & Sauran Cibiyoyin Kuɗi. Daga baya kuma aka naɗa shi mataimakin shugaban kwamitin ƙasafin kuɗi na majalisar dattawa.[1] A wani nazari na tsakiyar wa’adi na Sanatoci a cikin watan Mayun shekara ta 2009, ThisDay ya ce bai ɗauki nauyin wani ƙudiri a shekarar da ta gabata ba kuma bai bayar da gudunmuwar kaɗan ba a muhawarar.[3][4]

Maccido ya sake tsayawa takarar Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Arewa a zaɓen 26 ga watan Afrilun shekara ta 2011. Ya lashe Zaɓen ne da ƙuri’u 154,932, inda kuma ya ke gaban sauran ƴan takara 18.[2]

Manazarta

gyara sashe