Ahmed Hassan Barata

Mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

Ahmed Hassan Barata ya kasance dan siyasar Najeriya da aka zaba a matsayin dan Majalisar dattijai, mai wakiltar Adamawa ta Kudu a Adamawa,Najeriya a zaben watan Aprilu ta shekara, 2011. Ya tsaya takara a karkashin inuwan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Ahmed Hassan Barata
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 6 ga Yuni, 2015 - Ahmad Abubakar
District: Adamawa South
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

29 Mayu 1999 - ga Yuni, 2003
District: Guyuk/Shelleng
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

An zabi Barata a matsayin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Guyuk/Shelleng a watan Mayu ta shekarar,1999; mukamin da ya rike har zuwa watan Mayu, 2003.[1]a kara tsayawa takara karo na biyu a mazabar shi, amma ya sha kayi a hannun James Audu Kwawo na Jam'iyyar Action Congress.[1]

Barata yaci zaben fidda gwani na jam'iyyar (PDP) a shekarar 2011 na shiyar Adamawa ta Kudu.Ta samu kuri'u 738, a inda ya kada sanata mai ci Grace Folasade Bent wanda yasamu kuri'u 406.[2] Bent, wacce ake tsammanin tasamu fifiko daga shugabannin jam'iyyar (PDP), daga bisani tayi da'awar samun nasaran lashe zaben na fidda gwani.[1]. Duk da cewa ana akan duba da'awarta, wani Alkali ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta canza sunan Barata daga jerin sunayen yan takara da na Bent.[3] Daga bisani hukumar zabe ta (INEC) tayi watsi da da'awar Bent, da kotun daukaka kara dake Abuja, da kuma mashawartan jam'iyyar (PDP).[1]

A zaben watan Aprilu na shekarar 2011, Barata ya lashe zaben da kuri'u 101,760, akan abokin takaransa Mohammed Koiraga Jada na Jam'iyyar Action Congress of Nigeria mai kuri'u 66,525.[4]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 https://peoplepill.com/people/ahmed-hassan-barata
  2. Joe Nwankwo (7 March 2011). "Adamawa South - Opponent Wants Court to Delist Folasade Bent". Daily Independent. Retrieved 2011-05-06.
  3. Emmanuel Ogala (February 16, 2011). "Court orders electoral body to endorse three senators". Next. Retrieved 2011-05-06.[permanent dead link]
  4. "Collated Senate results". INEC. Archived from the original on 2011-04-19. Retrieved 2011-05-06.