Adamu Ncahama Baba-Kutigi
Farfesa Adamu Ncahma Baba-Kutigi ( An haifeshi ranar 10 ga watan Yunin shekarar 1956), a Kutigi, ƙaramar hukumar Lavun, a jihar Neja. Ya kasance tsohon shugaban riƙo na jami'ar tarayya ta Dutsinma.
Adamu Ncahama Baba-Kutigi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kutigi, 10 ga Yuni, 1956 (68 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Ƙabila | Mutanan nupe |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Usmanu Danfodiyo Jami'ar Ahmadu Bello |
Harsuna |
Turanci Hausa Nupenci |
Sana'a | |
Sana'a | author (en) da Malami |
Employers | Jami'ar Taraya dake Dutsinma (ga Maris, 2019 - Oktoba 2019) |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Rayuwar farko
gyara sasheAn kuma haifi Baba-Kutigi ranar 10 ga Yuni 1956 a Kutigi ga dangin Nupe. Ya yi karatun firamare a Sakandaren Gwamnati Eyagi, Bida, Jihar Neja. Ya samu takardar shedar karatun sa ta Najeriya (NCE) a kwalejin horar da malamai ta Minna wadda a yanzu ake kira da, Kwalejin ilimi ta Minna, a shekarar 1979. Ya kuma halarci tsohuwar jami'ar Sokoto, yanzu haka Jami'ar Usman Danfodio, inda kuma daga nan ya samu digiri na farko a fannin kimiyyar lissafi sannan ya sami digiri na biyu a fannin kimiyyar lissafi daga ABU Zaria.
Yana da kuma gogewa wajen koyarwa da bincike, kuma memba ne a ƙungiyar Malaman Kimiyya ta Najeriya (STAN), Cibiyar Nazarin Kimiyya ta Najeriya (NIP) da kuma a ƙungiyar Malaman Fasaha ta Najeriya (NATT). Ya yi aiki a matsayin Mataimakin Darakta, Cibiyar Nazarin Farko da Ƙarfafa ɗabi'a kuma a matsayin memba a Majalisar Mulki mai wakiltar Ikilisiya a Jami'ar Fasaha ta Tarayya ta Minna. [1]
A matsayin Shugaban Jami'a
gyara sasheMajalisar gudanarwar Jami’ar Tarayya ta Dutsinma, Katsina, ta kuma amince da naɗin Farfesa Adamu Nchama Baba-Kutigi a matsayin sabon mataimakin shugaban jami’ar. Hakan ya biyo bayan naɗin da majalisar dattawan da jami’ar ta yi a taron gaggawa karo na 73 da aka gudanar a watan Maris ɗin shekarar 2019. Kafin naɗin, Prof. Nchama Baba-Kutigi ya kasance tsohon shugaban tsangayar kimiyya na nan take, kuma shi ne tsohon shugaban sashen nazarin kimiyyar lissafi a jami’ar. [2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Baba-Kutigi "Baba-Kutigi the new VC Fudma. retrieved 26 June 2019. Independent
- ↑ FUDMA News "Federal University Dutsinma get acting vice chancellor" Archived 2019-06-26 at the Wayback Machine retrieved 26 June 2019. Daily Trust