Adam Thomas Lewis (an haife shi a ranar 8 ga watan Nuwamba shekara ta 1999) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na kasar Ingila wanda ke taka leda a matsayin dan kwallon gefen hagu.

Adam Lewis
Rayuwa
Cikakken suna Adam Thomas Lewis
Haihuwa Liverpool, 8 Nuwamba, 1999 (25 shekaru)
ƙasa Birtaniya
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Liverpool F.C.2019-
 
Muƙami ko ƙwarewa fullback (en) Fassara

Farkon rayuwarsa

gyara sashe

An haifi Lewis a Liverpool, Merseyside . [1]

Ayyukan kulob dinsa

gyara sashe

Liverpool

gyara sashe

Lewis ya sanya hannu kan kwangila na dogon lokaci tare da kungiyar Liverpool a watan Fabrairun 2019 [2] kuma ya fara buga wasan farko a ranar 4 ga Fabrairu 2020 a wasan FA Cup zagaye na hudu da Shrewsbury Town. [3][4]

Amiens (zuwa matsayin aro)

gyara sashe

Lewis ya shiga kungiyar Ligue 2 ta Faransa Amiens a kan aro don kakar 2020-21.[5]

Plymouth Argyle

gyara sashe

A ranar 14 ga watan Janairun 2021, Lewis ya koma Ingila don shiga kungiyar EFL League One ta Plymouth Argyle a kan aro har zuwa karshen kakar 2020-21. [6] Ya saka kwallaye na farko ga Argyle a ranar 19 ga watan Janairu, a karon farko da ya yi wa kulob din.[7]

Livingston

gyara sashe

A ranar 10 ga watan Yunin 2021, Lewis ya koma kungiyar Livingston na Scotland a kan yarjejeniyar aro na tsawon lokaci.[8][9]

Zuwansa Newport County

gyara sashe

A ranar 23 ga watan Yunin 2022, Lewis ya koma kungiyar EFL League Two ta Newport County a kan aro dominn kakar 2022-23. [10] Ya fara bugawa Newport wasa a ranar 6 ga watan Agusta 2022 a matsayin mai maye gurbin rabi na biyu a wasan 1-0 na League Two da aka yi wa Walsall.[11]

Lewis ya zira kwallonsa ta farko ga Newport a 1-1 League Two draw a kan Rochdale a ranar 7 ga Janairun 2023.[12] An yanke rancensa a Newport a ranar 25 ga Fabrairu 2023 ta hanyar raunin da ya ƙare.[13] A watan Yulin 2023 Lewis ya koma Newport County a kan aro lokacin kakar 2023-24. [14]

A ranar 5 ga Yuni 2024, an ba da sanarwar cewa Lewis zai bar Liverpool saboda zuwan ƙarshen kwangilarsa a ƙarshen watan. [15]

Morecambe

gyara sashe

Lewis na ɗaya daga cikin mutane 15waɗanda suka sanya hannu a kulob din Morecambe na League Two a ranar 12 ga Yulin 2024, bayan an ɗaga takunkumin da aka saka ma kulob din kan yin rajistar sabbin 'yan wasa.[16]

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

Lewis ya wakilci tawagar Ingila ta kasa da shekaru 16 a wasansu da Scotland a shekarar 2014. [17] Ya kasance memba na tawagar da ta fafata a gasar zakarun Turai ta kasa da shekaru 19 ta 2018 kuma daga baya a wannan shekarar ya fara bugawa tawagar kasa da shekaru 20. [18][18]

Ya kasance memba na tawagar da ta fafata a gasar zakarun Turai ta kasa da shekaru 19 ta 2018 kuma daga baya a wannan shekarar ya fara bugawa tawagar kasa da shekaru 20. [19][19]

Kididdigar aiki

gyara sashe
kididdiga
Club Season League National Cup League Cup Other Total
Division Apps Goals Apps Goals Apps Goals Apps Goals Apps Goals
Liverpool U21 2019–20 1 0 1 0
Liverpool 2019–20 Premier League 0 0 1 0 0 0 0 0 1 0
2020–21 Premier League 0 0 0 0 0 0 0 0 0 0
2021–22 Premier League 0 0 0 0 0 0 0 0 0 0
2022–23 Premier League 0 0 0 0 0 0 0 0 0 0
Total 0 0 1 0 0 0 0 0 1 0
Amiens (loan) 2020–21 Ligue 2 9 0 0 0 0 0 9 0
Plymouth Argyle (loan) 2020–21 League One 20 1 0 0 0 0 0 0 20 1
Livingston (loan) 2021–22 Scottish Premiership 9 0 0 0 5 0 14 0
Newport County (loan) 2022–23 League Two 21 1 1 0 3 0 3 0 28 1
Career total 59 2 2 0 8 0 4 0 73

Manazarta

gyara sashe
  1. "Adam Lewis: Profile". worldfootball.net. HEIM:SPIEL. Retrieved 7 September 2020.
  2. "Adam Lewis commits his future to Liverpool FC". Liverpool F.C. 19 February 2019. Retrieved 5 February 2020.
  3. "Liverpool vs. Shrewsbury Town – 4 February 2020". Soccerway. Perform Group.
  4. "Adam Lewis' reaction to LFC debut and Anfield crowd". Liverpool F.C. 6 February 2020. Retrieved 19 August 2020.
  5. "Adam Lewis joins Amiens SC on loan". Liverpool F.C. 18 August 2020. Retrieved 19 August 2020.
  6. "Adam Lewis Signs". Plymouth Argyle FC. 14 January 2021. Retrieved 14 January 2021.
  7. @Only1Argyle. (Tweet) https://twitter.com/ – via Twitter. Missing or empty |title= (help)
  8. "Adam Lewis swaps Liverpool for Livingston". livingstonfc.co.uk. 10 June 2021.
  9. "Adam Lewis: Liverpool left-back joins Livingston on loan". BBC Sport. 10 June 2021. Retrieved 10 June 2021.
  10. Lewis Newport loan
  11. Lewis Newport debut
  12. Lewis first Newport goal
  13. Lewis loan ended
  14. Lewis rejoins Newport
  15. "LFC confirms Premier League retained list and departures". www.liverpoolfc.com. 5 June 2024. Retrieved 5 June 2024.
  16. "Morecambe: League Two side make 15 signings after embargo lifted". BBC Sport (in Turanci). 2024-07-12. Retrieved 2024-07-13.
  17. "England U16s see off Scotland in Victory Shield encounter". The Football Association. 20 November 2014. Retrieved 19 August 2020.
  18. 18.0 18.1 "Adam Lewis commits his future to Liverpool FC". Liverpool F.C. 19 February 2019. Retrieved 5 February 2020.
  19. 19.0 19.1 "Adam Lewis commits his future to Liverpool FC". Liverpool F.C. 19 February 2019. Retrieved 5 February 2020.