Adamu Abu Kasim ƙwararre ne a fannin ilmin tsirrai na Najeriya kuma farfesa a fannin kimiyya.[1] Abubakar Sani Bello ya naɗa shi mataimakin shugaban jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida da ke Lapai a watan Disambar shekara ta, 2019.[2][3][4]

Abu Kasim Adamu
mutum
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Wurin haihuwa Jihar Neja
Sana'a mataimakin shugaban jami'a, Farfesa da botanist (en) Fassara
Filin aiki Botany da Ilimin kimiyyar noma
Ilimi a Jami'ar Ahmadu Bello da Jami'ar Najeriya, Nsukka
hoton abu kasim
hoton Abu kasim

An haife shi Dukku dake Rijau a Jihar Neja a can ya fito. Ya yi makarantar farko a shekarar 1980 inda ya halarci Makarantar Sakandare ta Tsakiya Dukku bayan ya kammala karatunsa na sakandare a shekarar, 1985 zuwa 1987 a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati. Kagara. Daga nan sai ya wuce Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya ta Jarrabawar Hukumar Haɗin Gwiwa ta wucin gadi da aka fi sani da (IJMB) sannan a shekarar, 1989 ya samu digirin digirgir a fannin ilimin Botany a Jami’ar Ahmadu Bello inda ya kammala digiri na biyu.[5]

Ya kuma yi digirin digirgir (M.Sc) na Botany da Digiri na uku a fannin amfanin gona a jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya sannan ya samu takardar shedar karatu a fannin Tissue Biotechnology a shekarar, 1995 a jami'ar Najeriya dake Nsukka.[6]

Ƙungiyar membobin da aka gudanar sun haɗa da:[7]

  • Ƙungiyar Halitta ta Najeriya
  • Ƙungiyar Malamai ta Najeriya
  • Ƙungiyar Ƙwararrun Ƙwararru da Kimiyya ta Ƙasa
  • Botanical Society of Nigeria.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-15. Retrieved 2023-03-15.
  2. https://ibabanaija.com.ng/2019/12/10/prof-abu-kasim-adamu-is-ibbul-new-vice-chancellor/[permanent dead link]
  3. https://www.blueprint.ng/well-make-ibbul-centre-of-academic-excellence-vc/
  4. https://educeleb.com/ibbu-gets-new-vice-chancellor/
  5. https://newnigeriannewspaper.com/2019/12/11/prof-adamu-emerges-ibb-university-lapai-vc/[permanent dead link]
  6. http://ibbu.edu.ng/the-vice-chancellor/
  7. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-09-20. Retrieved 2023-03-15.