Abdul-ƙadir Kure
An haifi Abdulkadir Kure a garin Lapai da ke jihar Neja a Najeriya a ranar 26 ga Fabrairu, 1956. Ya yi gwamnan jihar Neja tsakanin 1999 zuwa 2007
Abdul-ƙadir Kure | |||
---|---|---|---|
29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007 ← Habibu Idris Shuaibu - Mu’azu Babangida Aliyu → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Lapai, 26 ga Faburairu, 1956 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mutuwa | Jamus, 8 ga Janairu, 2017 | ||
Yanayin mutuwa | (cuta) | ||
Karatu | |||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci | ||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Karatu
gyara sasheKure ya yi karatun a fannin civil engineering jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, kuma ya kammala digirinsa na farko a shekarar 1976, ya yi NYSC a jihar Benuwe daga 1976-1977, Kure ya fara aiki da ma'aikatar ayyuka ta jihar Neja a matsayin dalibin injiniyan kafin yaci gabada karatun Masters a University of Newcastle, United Kingdom,1981
Aiki da Siyasa
gyara sasheBayan kammala karatunsa, Kure ya koma ma’aikatan gwamnati na jihar Neja, daga baya kuma ya bar aikin hukumar raya babban birnin tarayya Abuja a matsayin babban injiniya a shekarar 1985. Ya yi ritaya daga FCDA a shekarar 1995 a matsayin director of engineering.
Siyasa
gyara sasheKure ya kasance dan jam’iyyar PDP, wanda a karkashinta ya yi gwamnan jihar Neja daga 1999 zuwa 2007. Ya kasance mai kare shari’ar Musulunci kuma ya kasance gwamna na biyu bayan Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmed Sani Yerima. gabatar da dokar a Najeriya a watan Mayun 2000. Hakan baiyiwa Kiristocin jihar dadi ba domin suna gani hakan kamar wata hanyace ta mayar dasu Saniyar ware.
Bayan karewar wa'adin mulkinsa shugaban kasa Umaru 'Yar'aduwa ya nada shi shugaban hukumar kula da tituna ta tarayya (FERMA) inda ya yi aiki har zuwa shekarar 2010. Tsohon gwamnan ya kasance dan jam'iyyar PDP mai kishin kasa. Ya kasance wakili a babban taron kasa na 2014 da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kira. Ya kuma kasance wanda bai fito fili ya yi tunanin komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba a cikin zazzafar gudun hijirar ‘ya’yan Jam'iyyar PDP suke zuwa jam’iyya mai mulki a yanzu.[1]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheKure ya auri Zainab Abdulkadir Kure, tsohuwar ma’aikaciyar gwamnati tun shekarar 2007 tana ‘yar majalisar dattawan Najeriya. su n haifi mata biyu mata da maza hudu.[2]
Mutuwa
gyara sasheKure ya rasu ne a ranar 8 ga Janairu, 2017 a kasar Jamus inda ya je neman magani.[3]