Zubairu Dada

Ɗan siyasan Najeriya

Zubairu Dada [1][2](an haifeshi ne a ranar 28 ga watan Maris, shekara ta alif dari tara da hamsin da biyu 1952 a Minna, Jihar Neja.[3]

Zubairu Dada
Minister of State for Foreign Affairs of Nigeria (en) Fassara

21 ga Augusta, 2019 - 2023
Khadija Bukar Ibrahim
Rayuwa
Haihuwa 28 ga Maris, 1952 (72 shekaru)
Sana'a

Karatu gyara sashe

Yayi makarantar firamare a Minna, daga shekara ta alif dari tara da hamsin da takwas 1958 zuwa shekara ta alif dari tara da sittin da hudu 1964 Ya kammala karatun Turanci da Faransanci a jami'ar Ahmadu Bello zaria 1974 sannan ya yi digirin digirgir a fannin shari’a da diflomasiyya a Jami’ar Jos a shekara ta alif ɗari tara da casa'in 1990.[4]

Ayyuka gyara sashe

Ya fara aiki a matsayin jami'in yada labarai a shekarar 1975 a jihar Arewa maso yamma sannan ya kai matsayin babban sakatare a shekarar 1986. Sannan ya kasance darakta na MAMSER (Mass Mobilisation for Self Reliance, Social Justice, and Economic Recovery) daga alif dari tara da casa'in da biyu 1992. Zuwa alif dari tara da casa'in da uku 1993 da Darakta, National Orientation Agency (NOA) daga alif dari tara da casa'in da uku 1993-Uwa alif dari tara da casa'in da tara 1999.[5]

Jakada gyara sashe

An nada shi jakadan Najeriya a kasar Poland daga shekarar alif ɗari tara da casa'in da tara 1999 zuwa shekara ta dubu biyu da uku 2003 da kuma babban kwamishinan Najeriya a jamhuriyar Mozambique tare da samun karbuwa a jamhuriyar Madagascar daga shekara ta dubu biyu da huɗu 2004 zuwa shekara ta dubu biyu da bakwai 2007. Har zuwa lokacin da aka nada shi Minista, ya yi Kwamishinan kudi da Tattalin Arziki a shekara ta dubu biyu da goma sha ɗaya 2011 zuwa shekara ta dubu biyu da goma sha shida – 2016.[6]

Minista gyara sashe

A shekarar 2019 shugaba Muhammadu Buhari ya nadashi a matsayin Karamin Ministan Harkokin Waje, [7][8][9]kuma memba a Cibiyar Gudanarwa ta Najeriya (NIM) da Cibiyar Hulda da Jama'a ta Najeriya (NIPR).[10] Ya rike sarautar gargajiya ta Makun Paiko.

Manazarta gyara sashe

  1. "Minister of State Foreign Affairs Ambassador Zubairu Dada Archives". FRCN (in Turanci). Retrieved 2020-09-16.
  2. "Reverse Appointment Of Ambassador Zubairu Dada – Niger APC | Channels Television". www.channelstv.com. Retrieved 2020-10-06.
  3. "Nigeria needs MAMSER now more than ever, says ministerial nominee, Dada". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2020-10-06.
  4. https://abuja.mfa.gov.hu/eng/news/latogatas-zubairu-dada-kueluegyminiszter-helyettesnel
  5. https://punchng.com/tags/zubairu-dada/
  6. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-12-04. Retrieved 2021-12-04.
  7. "FULL LIST: Portfolios of Buhari's 44 Ministers - 2019 - 2023" (in Turanci). 2019-08-21. Retrieved 2020-09-16.
  8. Iroanusi, QueenEsther (2019-07-23). "Nigeria: Buhari appoints Akpabio, Keyamo, Fashola, 40 other ministers (FULL LIST)". allAfrica.com (in Turanci). Retrieved 2020-09-17.
  9. "Ambassador Zubairu Dada visits ECOWAS headquarters over fire outbreak". Vanguard News (in Turanci). 2020-08-06. Retrieved 2020-10-06.
  10. https://www.premiumtimesng.com/features-and-interviews/347874-for-the-record-official-citations-of-buharis-ministers-sgf.html