Zirnaƙo wani ƙwaro ne daga cikin ƙwari masu cizo yana kama da rina ko zanzaro amma yafi kama da rina saboda koda gidan su kusan kala ɗaya da na rina sai dai yafi rina girma sannnan shi Zirnaƙo baƙi ne ana kiranshi da turanci da (Black hornet) yana yin gidanshi kalan na rina sai dai nashi yafi na rina girma yakanyi a bishiya babba da ƙarami ko kuma a cikin irin ɗakunan ƙauye can sama a jinka.[1] Zirnaƙo yana da zafi a yayin da ya ciza mutum yakan zuba ma mutane wani ruwan dafi mai mugun zafi! Wani lokaci wajen da ya ciza har kumburi yakeyi wajen sai yayi ja. Saɓanin Zuma ita ƙari take amfani dashi.

Zirnaƙo
Scientific classification
KingdomAnimalia
PhylumArthropoda
Classinsect (en) Insecta
OrderHymenoptera (mul) Hymenoptera
DangiVespidae (en) Vespidae
Genushornet (en) Vespa
jinsi Vespa basalis
,

Sassan da ake samun Zirnaƙo

gyara sashe

Ana samun Zirnaƙo a sassa daban daban na duniya har ma Najeriya da wasu yankunan Afirka Zirnaƙo kusan jinsunan 5,000 a faɗin duniya.

Gabatar dashi

gyara sashe

Waɗansu ƙasashen su Burtaniya, Kolombiya da sauransu dukkan su kai zirnaƙo akayi a can a cikin shekarar 2019. Yana tasowa daga gidan shi don ya harbi mutane, wani kuma sai dai idan an tokalo shi. Banbancin shi da rina daga girma sai launin jikin su.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Zirnaƙo". Hausadictionary.com. 11 March 2019. Retrieved 11 September shekarar 2021. Check date values in: |accessdate= (help)