Makhdoomzada Muhammad Zain Hussain Qureshi ( Urdu: مخدوم زادہ محمد زین حسین قریشی‎ ) ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya kasance memba a Majalisar DDokokin kasar Pakistan tun daga watan Agustan shekarar 2018 zuwa watan Afrilun shekarar 2022. Ya kuma kasance memba na Majalisar Lardi na Punjab daga watan Yulin shekarar 2022 zuwa watan Janairun shekarar 2023.

Zain Qureshi
Member of the 15th National Assembly of Pakistan (en) Fassara

18 ga Yuli, 2022
District: NA-157 Multan-IV (en) Fassara
Rayuwa
ƙasa Pakistan
Harshen uwa Urdu
Ƴan uwa
Mahaifi Makhdoom Shah Mahmood Hussain Qureshi
Karatu
Harsuna Urdu
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Pakistan Tehreek-e-Insaf (en) Fassara

Fagen siyasa

gyara sashe

An zaɓi Qureshi a Majalisar Dokokin kasar Pakistan daga Mazaɓar NA-157 (Multan-IV) a matsayin ɗan takarar Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI) a babban zaɓen kasar Pakistan na shekarar 2018 .[1][2]

A ranar 27 ga watan Satumbar shekarar 2018, Firayim Minista Imran Khan ya naɗa shi Sakataren Kuɗi na Majalisar Tarayya.[3] Ya yi aiki har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2022, lokacin da ya yi murabus daga majalisar tare da sauran membobin PTI.

An zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar wakilai na lardin Punjab daga PP-217 Multan-VII a matsayin dan takarar PTI a zaɓen fidda gwani na lardin Punjab na shekarar 2022 . Ya yi rantsuwa a ranar 18 ga watan Yuli, shekarar 2022.

Yana neman kujera a Majalisar Lardi daga PP-217 Multan-VII a matsayin ɗan takarar PTI a zaɓen lardin Punjab na shekarar 2023 .[4]

Ɓangaren Aiki

gyara sashe

A cikin shekarar 2009, Qureshi ya shiga aiki a matsayin ɗan majalisa a ofishin Sanata John Kerry na Amurka.[5][6] Bayan zamansa a Amurka, ya yi aiki a matsayin manajan dangantaka a Bankin MCB daga shekarar 2009 zuwa ta shekarar 2012.

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Qureshi ɗa ne ga ministan harkokin wajen Pakistan Shah Mahmood Qureshi .[5]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Imran Khan's PTI on top as election results come in". Retrieved 26 July 2018.
  2. "LIVE UPDATES: PTI leads in election 2018 results". www.pakistantoday.com.pk. Retrieved 4 August 2018.
  3. "15 MNAs appointed as parliamentary secretaries". www.pakistantoday.com.pk. 27 September 2018. Retrieved 30 September 2018.
  4. "List of PTI Candidates for Provincial Elections In Punjab | 2023". Pakistan Tehreek-e-Insaf (in Turanci). 2023-04-19. Retrieved 2023-04-21.
  5. 5.0 5.1 "Pak FM's son served as Kerry's intern". The Daily Star. 21 October 2009. Retrieved 4 May 2020.
  6. Rajghatta, Chidanand (22 October 2009). "Pak minister faces criticism over son working for Kerry". Times of India. Retrieved 4 May 2020.