Zaben majalisar dattawan Najeriya na 2019 a jihar Kano

Zaɓen ƴan majalisar dattawan Najeriya na shekarar 2019 a jihar Kano da aka gudanar ranar 23 ga watan Fabrairu, shekarar 2019, domin zaɓen ƴan majalisar dattawan Najeriya da za su wakilci jihar Kano. Ibrahim Shekarau mai wakiltar Kano ta tsakiya, Jibrin I Barau mai wakiltar Kano ta Arewa da Kabiru Ibrahim Gaya mai wakiltar Kano ta kudu duk sun yi nasara a jam'iyyar All Progressives Congress.[1][2][3][4][5][6][7]

Infotaula d'esdevenimentZaben majalisar dattawan Najeriya na 2019 a jihar Kano
Iri zaɓe
Ƙasa Najeriya
Applies to jurisdiction (en) Fassara jihar Kano
Alaka Jam'iyya Jimilla
APC PDP
Kafin Zabe 2 1 3
Bayan Zabe 3 0 3

Takaitawa

gyara sashe
Gunduma Wanda yayi nasara Jam'iyya Zababben Sanata Jam'iyya
Kano ta Tsakiya Dr Rabiu Musa Kwankwaso PDP Ibrahim Shekarau APC
Kano ta Arewa Jibrin I Barau APC Jibrin I Barau APC
Kano ta Kudu Kabiru Ibrahim Gaya APC Kabiru Ibrahim Gaya APC

Kano ta Tsakiya

gyara sashe

Ƴan takara 30 ne suka yi rajista da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa domin yin takara a zaɓen. Ɗan takarar jam’iyyar APC Ibrahim Shekarau ne ya lashe zaɓen inda ya doke ɗan takarar jam’iyyar PDP Madaki Aliyu Sani da wasu ƴan takarar jam’iyyar 28. Shekarau ya samu kashi 61.60% na ƙuri’u, yayin da Aliyu Sani ya samu kashi 33.68.[8][9][10][11][12][13][14][15]

Kano ta Arewa

gyara sashe

Ƴan takara 28 ne suka yi rajista da hukumar zaɓe mai zaman kanta domin su fafata a zaben. Ɗan takarar jam’iyyar APC Jibrin I Barau ne ya lashe zaɓen inda ya doke ɗan takarar jam’iyyar PDP Ahmed Garba Bichi da wasu ƴan takarar jam’iyyar 26. Barau ya samu kashi 61.37% na ƙuri’u, yayin da Garba Bichi ya samu kashi 33.35%.[16][17][18][19]

Kano ta Kudu

gyara sashe

Ƴan takara 28 ne suka yi rajista da hukumar zaɓe mai zaman kanta domin su fafata a zaɓen. Ɗan takarar jam’iyyar APC Kabiru Ibrahim Gaya ne ya lashe zaɓen inda ya doke dan takarar jam’iyyar PDP Abdullahi Sani Rogo da wasu ƴan takarar jam’iyyar 26. Gaya ya samu kashi 55.39% na kuri'un, yayin da Rogo ya samu kashi 37.77%.[20][21][22]

Manazarta

gyara sashe
  1. "APC wins two Senatorial Seats in Kano". Latest Nigeria News, Nigerian Newspapers, Politics (in Turanci). 2019-02-25. Retrieved 2021-08-05.
  2. "GANDUJE COMMENDS KANO FOR ELECTING BUHARI, 3 SENATORS, 24 REPS MEMBERS FROM APC". Archived from the original on 2020-08-04.
  3. "List of all Senators elected in 2019 National Assembly elections". Pulse Nigeria (in Turanci). 2019-03-12. Retrieved 2021-08-27.
  4. "Election Centre". nigeriaelections.stearsng.com. Retrieved 2021-08-27.
  5. "ELECTED SENATORS FOR THE 9TH ASSEMBLY" (PDF). Archived (PDF) from the original on 2021-05-14.
  6. Jannah, Chijioke (2019-04-05). "Kano Senator vows to takeover Ekweremadu's job in Senate". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2021-08-27.
  7. "Nigerian Senator, Senators in Nigeria :: Nigeria General Information :: Nigeria Information & Guide". www.nigeriagalleria.com. Retrieved 2021-08-30.
  8. "Shekarau Defeats Madaki As APC Sweeps Kano Senatorial Race". Channels Television. Retrieved 2021-08-05.
  9. "Shekarau wins senatorial seat in Kano State". Punch Newspapers (in Turanci). 2019-02-25. Retrieved 2021-08-05.
  10. "Ex-Gov. Shekarau wins senatorial seat in Kano State". Vanguard News (in Turanci). 2019-02-25. Retrieved 2021-08-05.
  11. "INEC RESULT SHEET KANO SENATORIAL ELECTION 2019" (PDF). Archived (PDF) from the original on 2019-11-08.
  12. "Shekarau displaces Kwankwaso's proxy for Kano senatorial seat". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2019-02-27. Archived from the original on 2021-08-27. Retrieved 2021-08-27.
  13. Ukwu, Jerrywright (2019-03-19). "Election 2019: Shekarau, Ndume top senators with highest votes". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Archived from the original on 2021-08-27. Retrieved 2021-08-27.
  14. "Ex-Gov. Shekarau wins senatorial seat in Kano State - P.M. News" (in Turanci). Retrieved 2021-08-27.
  15. "Goje, Orji Kalu, Shekarau -- ex-govs elected as senators while facing corruption trials". TheCable (in Turanci). 2019-06-15. Retrieved 2021-08-27.
  16. "APC Wins Two Senatorial Seats in Kano". THISDAYLIVE (in Turanci). 2019-02-25. Retrieved 2021-08-05.
  17. "INEC RESULT SHEET KANO SENATORIAL ELECTION 2019" (PDF). Archived (PDF) from the original on 2019-11-08.
  18. "NG Election Archives". Businessday NG (in Turanci). Retrieved 2021-08-27.
  19. Nigeria, Ripples (2019-02-25). "APC clears Kano Senate seats as Shekarau wins Kano Central". Latest Nigeria News | Top Stories from Ripples Nigeria (in Turanci). Retrieved 2021-08-27.
  20. "Gaya, Jibrin retain senatorial seats". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 2021-08-05.
  21. "Confam INEC list of elected Nigeria Senators". BBC News Pidgin. Retrieved 2021-08-05.
  22. "IINEC RESULT SHEET KANO SENATORIAL ELECTION 2019" (PDF). Archived (PDF) from the original on 2019-11-08.