Yvonne Tsikata
Yvonne Tsikata masaniya ce a fannin tattalin arzikin Ghana kuma a halin yanzu tana aiki a matsayin mataimakiyar shugaban bankin duniya kuma sakataren kamfanoni. Ta taɓa zama shugabar ma’aikata kuma Darakta a ofishin shugabar rukunin bankin duniya.[1] Yvonne kuma ita ce darektar sashen Rage Talauci da Sashen Gudanar da Tattalin Arziki na Turai da Yankin Asiya ta Tsakiya.
Yvonne Tsikata | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ghana, 1963 (60/61 shekaru) |
Karatu | |
Makaranta |
Wesley Girls' Senior High School Bryn Mawr College (en) New York University (en) |
Sana'a | |
Sana'a | Mai tattala arziki |
Mahalarcin
| |
Employers |
New York University (en) United Nations University (en) Organization for Economic Cooperation and Development (en) Bankin Duniya |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheTsikata ta yi karatun sakandare a Wesley Girls' High School. Ta yi karatun digiri na farko a Kwalejin Bryn Mawr da ke Pennsylvania. Ta sami digiri na biyu a fannin tattalin arziki daga Jami'ar New York.[2]
Sana'a
gyara sasheYvonne ta fara aikinta a matsayin Malama na ka'idar kuɗi da ka'idar tattalin arziki a Jami'ar New York. Ta yi aiki da Kungiyar Haɗin Kan Tattalin Arziki da Ci Gaba a birnin Paris da kuma Cibiyar Bincike kan Tattalin Arzikin Duniya na Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya da ke Helsinki.[3]
Yvonne ta shiga rukunin Bankin Duniya a shekara ta 1991. Kafin ta shiga ofishin shugaban bankin duniya a watan Satumban 2013, Tsikata ta kasance Darakta mai kula da manufofin tattalin arziki a yankin Turai da tsakiyar Asiya.[4] Ta yi aiki a matsayin Daraktar ta Ƙasa na Caribbean a yankin Latin Amurka.[5][6] Ta ziyarci Haiti a madadin bankin duniya bayan girgizar ƙasa a ƙasar.[7][8]
A cikin shekarun 1998 da 2001, yayin da take hutu daga rukunin Bankin Duniya, ta yi aiki a matsayin babbar jami'in bincike a Cibiyar Nazarin Tattalin Arziki da Zamantakewa a Dar es Salaam, Tanzania; a matsayin mai ba da shawara ga Kungiyar Haɗin gwiwar Tattalin Arziki da Ci Gaba a Paris; da kuma zuwa Cibiyar Nazarin Ci gaban Tattalin Arziki ta Duniya na Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya da ke Helsinki.[9]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "World Bank, IMF officials pray for smooth event in Bali". The Jakarta Post (in Turanci). Retrieved 2019-03-02.
- ↑ "World Bank, IMF officials pray for smooth event in Bali". The Jakarta Post (in Turanci). Retrieved 2019-03-02.
- ↑ "Yvonne Tsikata: First shock of second wave of crisis not to affect Armenia". armenpress.am (in Turanci). Retrieved 2019-03-02.
- ↑ "Yvonne Tsikata, Intl Bank Reconstruction & Dev: Profile and Biography - Bloomberg Markets". Bloomberg.com. Retrieved 2020-11-14.
- ↑ Editor, Staff (2010-12-10). "Norway $$ can't be released until steering committee says so – World Bank". Stabroek News (in Turanci). Retrieved 2019-03-02.CS1 maint: extra text: authors list (link)
- ↑ "World Bank funds Dominican Republic's energy project". Devex. 2008-05-20. Retrieved 2019-03-02.
- ↑ "Jamaica receives US$10 million to restore basic community infrastructure in the aftermath of Hurricane Dean - Jamaica". ReliefWeb (in Turanci). Retrieved 2019-03-02.
- ↑ APO (2019-02-15). "World Bank and International Monetary Fund (IMF) Officials visit Morocco to prepare 2021 Annual Meetings in Marrakech". CNBC Africa (in Turanci). Archived from the original on 2019-03-06. Retrieved 2019-03-02.
- ↑ "Yvonne M. Tsikata's research works in Economics and Political Science". ResearchGate (in Turanci). Retrieved 2019-03-02.