Yusuf Suleiman

Alhaji Yusuf sulaiman Dan siyasa ne a Nigeria

Alhaji Yusuf Suleiman (An kuma haife shi a ranar 30 ga watan Junairu shekarar alif 1963) a Gusau dake jihar Zamfara, dake Arewacin Najeriya. ɗan siyasa ne a Najeriya, kuma jinin Usmanu Danfodiyo ne da ke Sokoto. Yayi aikin gwamnati kafin ya shiga siyasa.

Yusuf Suleiman
Minister of Sports (en) Fassara

ga Yuli, 2011 - 2 Disamba 2011
Ibrahim Bio - Bolaji Abdullahi
Minister of Transportation (en) Fassara

6 ga Afirilu, 2010 - ga Yuli, 2011
Ibrahim Bio - Audu Idris Umar
Rayuwa
Haihuwa Jahar Nasarawa Sokoto, 30 ga Janairu, 1963 (61 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a civil servant (en) Fassara
Yusuf Suleiman

Asali/Salsala

gyara sashe

An haifi Yusuf a garin Gusau dake jihar Zamfara, arewacin Najeriya. Mahaifin sa Alhaji Suleiman Isah dan Ibrahim jikan Sarki Aliyu Karami dan Muhammad Bello dan Shekh Usman bin Fodio.

Yayi karatunsa na degre a fannin Kasuwanci a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, a shekarar alif (1986), da Mastas a shekara (1989) duk a jami'a daya.

 
Yusuf Suleiman

Ya kuma halarci jami'ar Havard flagship, yayin da yayi karatu kan Privatization, the public Enterprises Management Program a shekara ta (1995). Ya halarci Kellog School of Management's Executive Development Program a shekara (2002). Jami'ar Havard Kenny School's Senior managers in government program a shekara ta (2001), Jami'ar Virginia Darden Graduate School of Business on Managing Critical Resources a shekara ta (2002), Cambridge Academy of Transport Shipping Insurance course a shekara ta (2002), Kellog Graduate School of Management Certificate in the soul of leadership Program, a shekara ta (2003).

A shekara ta (1986) ya fara aiki da gwannatin Sokoto, a yayin da ya rike kujeran darakta na jaha, ma'aikatu a shekara ta (1991). Kuma yayi aiki a wajaje da dama a matakin jiha da taraiya.

A shekara ta (1990) an kuma zaɓe shi a matsayin daracta mai zartarwa a National Meritime Authority of Nigeria, wanda yanzu ake Kiran ta da (NIMASA). A shekara ta (2003) ya ajiye kujeran yayin da ya tsaya takaran sanata, a karkashin jam'iyar People Democratic Party (PDP).

 
Yusuf Suleiman

A ranan (6 ga watan Aprailu shekarar 2010), ya kuma zama ministan zirga-zirga na taraiyan Najeriya lokacin mulkin shugaban kasa Goodluck Jonathan. Ya zama ministan Wasanni a shekara ta (2011) Kuma ya sauka a (watan Desamba, shekarar 2011), lokacin da ya yanke shawaran tsayawa takaran gwamna a jihar Sokoto.[1][2]


Kafin ya zama Minista, ya kuma kasance chairman of the Governing Council of the National Teachers' Institute,Kaduna (NTI). Ya zama chaiman (CEO) na Afro investors limited, Pravate Equity firm Kafin ya sauka daga kujeran minista, a shekara ta (2012). Dadi da Kari, yanzu shine shugaba mai zartarwa (CEO) na kampanin Gaspia n Oil and Gas Limited.



Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.vanguardngr.com/2011/12/sokoto-guber-jonathan-accepts-minister-of-sport%E2%80%99s-resignation/
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2010-04-13. Retrieved 2020-08-26.