Yusuf Demir ( Turkish: [juˈsuf deˈmiɾ] ; an haife shi ranar 2 ga watan Yuni na shekarar 2003) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Austriya wanda ke taka leda a matsayin dan wasan gaba ga kungiyar kwallon kafan Galatasaray na Turkiyya Süper Lig da kuma tawagar ƙasar Austria .

Yusuf Demir
Rayuwa
Haihuwa Vienna, 2 ga Yuni, 2003 (21 shekaru)
ƙasa Austriya
Karatu
Harsuna Jamusanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Austria national under-17 football team (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Tsayi 1.73 m
IMDb nm14045765
Yusuf Demir
Yusuf Demir

Aikin kulob

gyara sashe

Rayuwar farko

gyara sashe

An haifi Yusuf Demir a ranar 2 ga watan Yuni na shekarar 2003, a Vienna, Austria, ga iyayensa da suke 'yan asalin kasar Turkiyya, tare da tushen danginsa a Trabzon, Turkiyya.

Rapid Wien

gyara sashe

A ranar 26 ga watan mayu na shekarar 2019, ya rattaba hannu a kan kwantiragi na manya tare da kungiyar Rapid Wien.Demir ya Fara buga wasan sa na farko ne da kungiyar farko ta rapid wien a wasan da suka samu nasara da ci 3--0 da suka buga da kungiyar Admira a ranar 14 ga watan Disamba a shekarar 2019,a ranar 15 ga watan satumba na shekarar 2020 ne kuma,Demir ya saka kwallo a wasan da suka sha kashi da ci 2--1 a hannun gent a wasan samun gurbin gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, a lokacin da yana dan shekara 17, wata uku da kwana 13, ya kuma zama mafi karancin shekaru na wanda ya zura kwallo tun Gerd Wimmer a shekarar 1994, a shekaru 17, wata goma da kwanaki 27

Barcelona

gyara sashe

A watan Yulin shekarar 2021 ne, kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da daukar Demir a matsayin aro na tsawon kakar wasa daga Rapid Wien kan Yuro 500,000, tare da zabin zama na dindindin a nan gaba kan karin Yuro miliyan 10, amma idan dan wasan ya kai wasanni goma kulob din. zai zama wajibi sai ya dauke shi.

A ranar 23 ga watan Agusta, a shekarar 2021, Demir ya fara buga gasa da Athletic Bilbao . Ya zo ne a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasa Martin Braithwaite bayan mintuna 61, ya zama matashin dan wasan Barça na waje tun Lionel Messi (mai shekaru 17 da kwanaki 114) ya yi hakan a shekarar 2004.

A ranar 31 ga watan Agusta na shekarar 2021, Barcelona ta yi rajistar dan wasa Demir a La Liga a matsayin ɗan wasa na farko bayan an saita shi a baya don yin rajista a cikin ajiyar . An mika masa riga mai lamba 11 wadda Ousmane Dembélé ya rike a baya.

A ranar 13 ga watan Janairu na shekarar 2022, an daina lamunin, kuma Demir ya koma Austria.

Galatasaray

gyara sashe

A ran 8 ga watan Satumban shekarar 2022, ya sanya hannu kan kwangilar shekaru 4 tare da kungiyar kwallon kafa taGalatasaray . An sanar da cewa za a biya kudin canja wuri na €6,000,000 ga tsohuwar tawagar dan wasan, Rapid Wien .

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

Demir matashi ne na kasa da kasa na Austria. Ya yi karo da babbar tawagar kasar Ostiriya a 3–1 2022 na cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA a kan Tsibirin Faroe a ranar 28 ga Maris 2021.

Kididdigar sana'a

gyara sashe
Bayyanar da burin ta kulob, kakar da gasar
Kulob Kaka Kungiyar Kofin kasa Turai Sauran Jimlar
Rarraba Aikace-aikace Manufa Aikace-aikace Manufa Aikace-aikace Manufa Aikace-aikace Manufa Aikace-aikace Manufa
Rapid Wien II 2019-20 Yankin League Gabas 1 0 0 0 - - 1 0
Rapid Wien 2019-20 Bundesliga Austria 6 0 0 0 - - 6 0
2020-21 25 6 2 1 5 [lower-alpha 1] 2 - 32 9
2021-22 10 1 1 0 2 [lower-alpha 2] 0 - 13 1
Jimlar 41 7 3 1 7 2 - 51 10
Barcelona (loan) 2021-22 La Liga 6 0 0 0 3 [lower-alpha 3] 0 0 0 9 0
Jimlar sana'a 43 6 3 1 10 2 0 0 56 9
Fitowa da burin tawagar ƙasa da shekara
Tawagar kasa Shekara Aikace-aikace Manufa
Austria 2021 4 0
Jimlar 4 0

Manazarta

gyara sashe


Cite error: <ref> tags exist for a group named "lower-alpha", but no corresponding <references group="lower-alpha"/> tag was found