Yakubu Ochefu
Farfesa Yakubu Aboki Ochefu, dan marigayi Kanar Anthony Ochefu, shi ne sakataren kwamitin shugabannin jami’o’in Najeriya[1]. Farfesa ne a Tarihin Tattalin Arzikin Afirka da Nazarin Ci Gaban Jami'ar Jihar Benue tun 2003.[2] Ya kasance tsohon shugaban jami’ar jihar Benue, tsohon shugaban Jami’ar Kwararafa, jihar Taraba, Najeriya[3] kuma shugaban kungiyar tsofaffin daliban Jami’ar Calabar[4]. A watan Disamba 2022, an zabe shi a matsayin shugaban kungiyar tsofaffin daliban jami'o'in Najeriya. Littattafansa na ilimi suna kan buɗaɗɗen dandamalin albarkatu na ilimi ciki har da Academia.edu[5] kuma ya haɗa karatun Nazarin Tarihin Tsakiyar Najeriya / tare da Aliyu A. Idrees a 2002.[6]
Yakubu Ochefu | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Mai tattala arziki |
Manazarta
gyara sashe- ↑ kings. "Prof. Yakubu Ochefu (Secretary General CVC ) | CVC" (in Turanci). Retrieved 2019-12-11.
- ↑ admin (2017-10-17). "Historical Society of Nigeria Engages Prof Yakubu Ochefu, African Economic History". Intervention (in Turanci). Retrieved 2019-12-11.
- ↑ "World stage group" (in Turanci). Archived from the original on 2019-12-11. Retrieved 2019-12-11.
- ↑ "University Of Calabar Nigeria". www.unical.edu.ng. Retrieved 2019-12-11.
- ↑ Ochefu, Yakubu. "Yakubu A. Ochefu Profile" (in Turanci).
- ↑ Idrees, Aliyu Alhaji; Ochefu, Yakubu A (2002). Studies in the history of Central Nigeria area (in English). Lagos, Nigeria : CSS Ltd. ISBN 978-978-2951-58-8.CS1 maint: unrecognized language (link)