Yakin Damasak

Yaki tsakanin yan kungiyar Boko Haram da Sojojin kasar Najeriya da Chadi

Yakin Damasak Ya faru ne a ranar sha takwas 18 ga watan Maris shekara ta dubu biyu da sha biyar 2015 lokacin da sojojin Nijar da na Chadi suka kai wa 'yan Boko Haram hari a garin Damasak na Najeriya. An fatattaki ‘yan Boko Haram daga garin bayan kwashe kasa da kwana guda ana gwabza kazamin fada.[1] A ranar ashirin da huɗu 24 ga watan Nuwamba shekarar dubu biyu da sha huɗu 2014 ne kungiyar Boko Haram suka kwace iko da garin Damasak, kuma ikon na karkashinsu har zuwa karshen wannan yakin. A lokacin da aka kwato garin ya kasance ba kowa.[2] Farar hular da suka rage a cikin garin daga marasa lafiya sai tsofaffin da ba za su iya barin garin ba.[3] Bayan yakin sojojin Chadi sun kafa sansanoni a wajen garin sannan jiragen helikwafta na Chadi guda biyu 2 sun iso da wasu kayayyaki.[4]

Infotaula d'esdevenimentYakin Damasak
Map
 13°06′18″N 12°30′24″E / 13.105°N 12.5067°E / 13.105; 12.5067
Iri faɗa
rikici
Bangare na Rikicin Boko Haram
Kwanan watan 9 –  17 ga Maris, 2015
Ƙasa Najeriya
Participant (en) Fassara
sojojin a Yakin Damasak

Bayan nan

gyara sashe

A ranar ashirin 20 ga watan Maris, kwanaki biyu bayan yakin, sojojin Nijar da kuma na Chadi sun gano wani wakeken kabari da mutane fiye da casa'in 90 aciki a karkashin wata gada dake a wajen birnin.[5][6] Gawarwakin fararen hular sun ji raunika ta hanyar iska ta hamada, wanda ke nuni da cewa an yi kisan kiyashi ne a wani lokaci da ya wuce.[7]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Soldiers drove the terrorists out of Damasak in Borno state [PHOTOS]". Pulse Nigeria (in Turanci). 2015-03-20. Retrieved 2021-01-14.
  2. "Boko Haram was 'driven out' of the northeastern Nigerian town". www.aljazeera.com (in Turanci). Retrieved 2021-01-14.
  3. "'Mass graves' were discovered". France 24 (in Turanci). 2015-03-21. Retrieved 2021-01-14.
  4. "Troops from Chad. Niger freed the Nigerian town from Boko Haram | The Seattle Times". 2015-04-02. Archived from the original on 2015-04-02. Retrieved 2021-01-14.
  5. Aminu Abubakar and Melissa Gray (21 March 2015). "Mass grave found in former Boko Haram-held town". CNN. Retrieved 2021-01-14.
  6. "Mass grave found in recaptured Nigerian town". www.aljazeera.com (in Turanci). Retrieved 2021-01-14.
  7. "Soldiers from Niger and Chad discover at least 70 victims of Boko Haram". Washington Post (in Turanci). ISSN 0190-8286. Retrieved 2021-01-14.