Kisan kiyashi a Damasak

Kisan gilla a garin Damasak da yan kungiyar Boko haram tayi, biyo bayan karbe iko da garin

Kisan kiyashi na Damasak ya kasance jerin kisan kiyashi ne da ƙungiyar Boko Haram ta yi a birnin Damasak na Najeriya.

Kisan gilla a Damasak
Wuri
Map
 13°06′18″N 12°30′24″E / 13.105°N 12.5067°E / 13.105; 12.5067

A ranar 24 ga watan Nuwamban shekara ta 2014 ne ƴan ƙungiyar Boko Haram ta mamaye birnin Damasak na Najeriya tare da kwace birnin a matsayin ramuwar gayya ga fararen hula da ke shiga ƙungiyoyin kare kai. Mazauna birnin sun tsere daga mayakan Boko Haram da ke ci gaba da samun nasara. Kimanin fararen hula 3,000 ne suka bar birnin suka tsere zuwa makwabciyar ƙasar Najeriyar wato Nijar. Sun tsallaka kogin Yobe da ke kan iyakar ƙasashen biyu a cikin jirgi ruwa ko kwale-kwale, wasu fararen hula da dama sun mutu a yayin yunƙurin su na yin iyo ta cikin kogin na Yobe. Boko Haram sun fara farautar mutanen da ke tserewa daga birnin suna kashe su, a karshen harin da aka kai an kashe mutane 50.[1]

Iko da yankin

gyara sashe

Ƴan Boko Haram sun mamaye garin na tsawon watanni hudu, a cikin waɗannan watanni huɗu mayakan Boko Haram sun aiwatar da kisan gilla a cikin birnin Damasak da kewayen sa. An kashe mutane 70-100, wanda aka fille kansu a ƙarƙashin wata gadar siminti da ke fitowa daga cikin birnin.[2][3] An kuma kashe wasu ɗaruruwa a gabar kogin da ya bushe da kuma wasu sassan garin. Ya zuwa karshen mamayar a ranar 17 ga watan Maris 2015, yan Boko Haram sun kashe fararen hula 400.[4]

A ranar 17 ga watan Maris na shekara ta 2015, sojojin Nijar da Chadi sun ƙaddamar da farmakin kwato birnin Damasak. Sojoji sama da 2,000 na Najeriya da na Chadi sun kai hari garin tare da kwato shi. yakin ya yi sanadin lalata motocin Boko Haram da dama tare da kashe mayakan Boko Haram 228.[5]

Duba kuma

gyara sashe

Yakin Damasak

Manazarta

gyara sashe
  1. "Nigeria: 50 dead in Boko Haram's attack on Damasak on Monday". ladepeche. 28 November 2014. Retrieved 26 January 2022.
  2. "'Mass grave' discovered in Nigerian town recaptured from Boko Haram". France 24. 21 March 2015. Retrieved 26 January 2022.
  3. "Mass grave found in former Boko Haram-held town in Nigeria". CNN. 20 March 2015. Retrieved 26 January 2022.
  4. "400 Murdered In Damasak Massacre, Buried In Mass Graves". Sahara reporters. 29 April 2015. Retrieved 26 January 2022.
  5. "Troops from Chad, Niger retake Nigerian town from Boko Haram". the Seattle Times. 18 March 2015. Archived from the original on 2 April 2015. Retrieved 26 January 2022.