Vincent Oppong Asamoah

Dan siyasan Ghana

Vincent Oppong Asamoah (an haife shi a watan Janairu 13, 1966) ɗan siyasan Ghana ne kuma memba na Majalisar Takwas na Jamhuriya ta huɗu ta Ghana.[1] Ya wakilci mazabar Dormaa ta Yamma a yankin Brong-Ahafo a kan tikitin jam'iyyar National Democratic Congress.[2][3] Shi ne tsohon mataimakin ministan matasa da wasanni na Ghana.[4][5][6][7][8]

Vincent Oppong Asamoah
Member of the 8th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2021 -
District: Dormaa West Constituency (en) Fassara
Election: 2020 Ghanaian general election (en) Fassara
Member of the 6th Parliament of the 4th Republic of Ghana (en) Fassara

7 ga Janairu, 2013 - 6 ga Janairu, 2017
District: Dormaa West Constituency (en) Fassara
Election: 2012 Ghanaian general election (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Nsoatre (en) Fassara, 13 ga Janairu, 1966 (58 shekaru)
ƙasa Ghana
Karatu
Makaranta Kwame Nkrumah University of Science and Technology Executive Master of Business Administration (en) Fassara : public administration (en) Fassara
University of Cape Coast
(1999 - Bachelor of Arts (en) Fassara : social work (en) Fassara
Harsuna Turanci
Bonol (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da social worker (en) Fassara
Wurin aiki Yankin Bono
Imani
Addini Kiristanci
Jam'iyar siyasa National Democratic Congress (en) Fassara

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Asamoah Kirista ne (Katolika). Yana da aure da ’ya’ya uku.[2]

Asamoah dan jam'iyyar National Democratic Congress (NDC) ne. A shekara ta 2012, ya tsaya takarar kujerar Dorma West a kan tikitin majalisar NDC ta shida na jamhuriya ta hudu kuma ya yi nasara.[2][9][10]

Kwamitoci

gyara sashe

Asamoah shi mamba a kwamitin ayyuka da gidaje sannan kuma mamba a kwamitin dabarun rage talauci.

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Asamoah a ranar 13 ga Janairu, 1966. Ya fito ne daga Nsoatre a yankin Bono a Ghana. Har ila yau, ya sami digiri na MBA a fannin Gudanar da Jama'a daga Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah, da BA daga Jami'ar Cape Coast.[2]

 
Vincent Oppong Asamoah

Asamoah ma'aikacin zamantakewa ne kafin ya tsaya takarar mukamin siyasa a 2012. Ya yi aiki a OLAM Ghana limit a Asawinso a yankin Yamma. An nada shi shugaban karamar hukumar Dormaa daga ranar 29 ga Afrilu 2009, har zuwa lokacin da aka rantsar da shi a matsayin dan majalisa a majalisar dokoki ta shida na jamhuriyar Ghana ta hudu a ranar 7 ga Janairu 2013.[2][11]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Parliament of Ghana".
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 "Ghana MPs - MP Details - Asamoah, Vicent Oppong". www.ghanamps.com. Retrieved 2020-02-09.
  3. Ghana, News (2016-03-06). "Defend and obey the electoral laws - Minister". News Ghana (in Turanci). Retrieved 2020-07-26.
  4. "'Disastrous' Ghana's deputy sports minister Vincent Oppong Asamoah loses in Dorma West Parliamentary election". GhanaSoccernet (in Turanci). Retrieved 2020-07-26.
  5. "Ghanaians vilify me anytime I talk about the Black Stars - Hon Vincent Oppong Asamoah". Footballghana (in Turanci). Retrieved 2020-07-26.
  6. Quao, Nathan. ""We spend $1 million on Black Stars away matches"- Deputy Sports Minister | Citi Sport" (in Turanci). Archived from the original on 2020-07-26. Retrieved 2020-07-26.
  7. Quao, Nathan. "Sports Ministry unhappy with GFA over friendlies | Citi Sport" (in Turanci). Archived from the original on 2020-07-26. Retrieved 2020-07-26.
  8. "Just do it, VOA and boss". Graphic Online (in Turanci). Retrieved 2020-07-26.
  9. "Vincent Oppong Asamoah accused of 'masterminding' Kwesi Appiah's sack as Ghana coach". www.ghanaweb.com (in Turanci). 2017-03-03. Retrieved 2020-07-26.
  10. "Sports Minister Nii Lante retains seat but Deputy Oppong Asamoah loses miserably". SportsWorldGhana (in Turanci). 2016-12-08. Retrieved 2020-07-26.
  11. "Dormaa intensifies HINI campaign". BusinessGhana. Retrieved 2020-07-26.