At A Gwankis event
Em-mustapha event

Iliyasu Umar gyara sashe

An haifeni a rana 1 ga watan Janairu,1997. Sunan mahaifina Umar. An haifeni a wani kyauye mai suna Kasso dake karamar hukumar Kajuru dake Kaduna Najeriya. Na kasance inason rubece rubuce da kuma bincike akan abunda ya shafi ilimi. Ni dalibi ne mai son karance karance da kuma son ganin mutane na neman ilimi. Mahaifiyata Zulaihatu Ibrahim yar asalin garin Tudun wada ce a kaduna.

Karatu gyara sashe

Na fara karatun framare a Kasso inda nakai matakin aji hudu, kafin daga bisani mahaifina yayi kaura ya dawo Kaduna, Unguwan Dosa da zama anan ne na cigaba da karatun framare har na kammala.

Bayan nan na wuce Kolejin tunawa da Sir Ahmadu Bello Sardauna dake Kaduna a inda na kamma karatun sakanadare na daga bisa ni nasamu gurbin karatu a Jami'ar Jihar Kaduna wato (Kaduna State University)dake Kaduna, a inda na karanci yadda kididdiga da ake lissafin kudi (Accounting).

Aiki gyara sashe

Bayan kammla karatu digiri na farko a jami'ar Jihar Kaduna na samu aiki da wata kamfani dake Kaduna mai reshe a Zaria mai suna (Leadway Assurance Company Ltd) a matsayin ma'aikaci mai bada shawara ga masu zuba hannun jari wato (financial advisor) bayan daina aiki dasu na koma kasuwanci da bincike da karatu da rubutu. A yanzu haka ni malami ne dake koyarwa a kolejin ilimi na gwamnati dake Soba a Kaduna.

Manazarta gyara sashe