Uche Ogah

Dan kasuwa a Najeriya

Uchechukwu Sampson Ogah[1] (an haife shi 22 Disamba 1969) tsohon ƙaramin ministan ma'adinai da ƙarafa na Najeriya ne.[2] Babban hamshaƙin ɗan kasuwa, mai saka jari kuma mai taimakon jama'a, Ogah shi ne shugaban kamfanin Master Energy Group,[3] wani kamfani mai rassa sama da 15 a masana'antu daban-daban, daga ciki akwai Masters Energy Oil and Gas Ltd. Ogah ya na riƙe da babbar lambar girmamawa ta Najeriya, ta Jami'in Hukumar Neja (OON) da kuma ta (Commander of the Order of Niger) (CON).[4][5] Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya zaɓe shi a matsayin minista, daga bisani kuma aka naɗa shi ƙaramin ministan ma’adinai da ƙarafa[6] a ranar Laraba, 21 ga Agusta, 2019, alokacin mulkin Buharin.[7][8][9]

Uche Ogah
Minister of State, Mines and Steel Development (en) Fassara

21 ga Augusta, 2019 - 13 Mayu 2022
Rayuwa
Haihuwa Abiya da Uturu (en) Fassara, 22 Disamba 1969 (54 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Mahaifi Wilson
Karatu
Makaranta Jami'ar Lagos
Jami'ar Najeriya, Nsukka
Jami'ar Olabisi Onabanjo
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa

Rayuwar farko da ilimi gyara sashe

An haifi Ogah ga Cif Wilson, mai kula da sha'anin tsafta kuma ma’aikacin layi dogo, yayi ritaya daga Ezinne Pauline Ogah[10] na Onuaku Uturu, ƙaramar hukumar Isuikwuato ta jihar Abia.[11]

Rayuwar iyali da aiki gyara sashe

Ogah ya auri Ngozi Sabina Ogah, wata mai sharhi kan harkokin kudi. Ogah ya kwashe shekaru 10 yana harkar banki. Ya fara da hidimar matasa ta kasa a NAL Bank PLC. Bayan haka, ya sami cikakken aiki a bankin (All States Trust Bank) kuma ya kwashe kimanin shekaru biyu a bankin kafin ya koma Bankin Zenith a shekarar 1997, inda ya kai matsayin Mataimakin Janar Manaja (AGM) kafin ya yi murabus a 2007.[10]

Tallafi gyara sashe

An ce ya samar da wutar lantarki a ƙauyukan Uturu, ya gina wa al’umma gidaje masu karimci, sannan ya gina babban ɗakin taro da ka iya daukar mutane 5,000 alokacin ɗaya, a jami’ar jihar Abia (ABSU) Uturu.[12]

Siyasa gyara sashe

Ogah ya tsaya takarar gwamnan jihar Abia, sau uku, na farko a ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Democratic Party da kuma jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki.

Tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya miƙa sunan Ogah a matsayin minista a ranar 23 ga Yuli, 2019 tare da wasu mutane 42 da aka naɗa.[13] A lokacin da yake tantance sanatoci a ranar 24 ga watan Yulin shekarar, ya bayyana tsare-tsarensa kan yadda zai yi aiki a kan matatun Najeriya[14] da kuma tsare-tsarensa na farashin kuɗin Najeriya.[15] Majalisar dattijai ta tabbatar da Ogah a matsayin minista a ranar 30 ga Yulin wannan shekara[16] kuma a ranar 21 ga Agusta, 2019 aka tabbatar da kuma rantsar da shi a matsayin ƙaramin ministan ma’adinai da ƙarafa.[17]

Manazarta gyara sashe

  1. "Uchechukwu Ogah: Champion Extraordinaire". THISDAYLIVE (in Turanci). 2019-04-28. Retrieved 2020-09-25.
  2. "About Ministers – Nigeria Mining Cadastre Office" (in Turanci). Retrieved 2022-02-15.
  3. "Masters Energy - Welcome to our World". Archived from the original on 2016-10-08. Retrieved 2023-12-05.
  4. "The 2014 National Award List" Archived 2014-10-02 at the Wayback Machine, ThisDayLive, 29 September 2014
  5. Ukanwa, Faith (2023-06-14). "Abia Rejoice Congratulates Uche Ogah On Receiving National Honours, CON" (in Turanci). Retrieved 2023-07-12.
  6. "JUST IN: Full List: Buhari assigns portfolios to new Ministers". Oak TV Newstrack. 21 August 2019. Archived from the original on 26 August 2019. Retrieved 26 August 2019.
  7. Nigeria, Daily News (2019-07-23). "Buhari New Ministers List 2019". Daily News Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 2020-04-24. Retrieved 2019-07-26.
  8. "FOR THE RECORD: Official citations of Buhari's ministers, SGF - Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2019-08-21. Retrieved 2022-06-21.
  9. Omokri, Reno (May 2, 2022). "2023: Uchechukwu Ogah Joins Abia Gubernatorial Race". THISDAYLIVE. Retrieved June 21, 2022.
  10. 10.0 10.1 "Uchechukwu Sampson Ogah biography, net worth, age, family, contact & picture". www.manpower.com.ng. Retrieved 2022-02-16.
  11. "Nigerian Biography: Biography Of Uchechukwu Sampson Ogah". www.nigerianbiography.com. Archived from the original on 2017-02-11.
  12. "CLOSE-UP: Who is Uche Ogah, the 'prayer warrior' otherwise known as Ikpeazu's nightmare?". TheCable (in Turanci). 2016-07-04. Retrieved 2022-02-15.
  13. "BREAKING: Amaechi, Akpabio, Akume, 40 others makes Buhari's 2019 ministerial list". Oak TV Newstrack. 23 July 2019. Archived from the original on 31 July 2019. Retrieved 31 July 2019.
  14. Television, Oak (24 July 2019). "Nigeria's 3 refineries can work again, Ministerial Nominee assures Senate". OAK TV. Archived from the original on 31 July 2019. Retrieved 31 July 2019.
  15. Television, Oak (24 July 2019). "Current value of naira is okay, Ministerial Nominee tells Senate". OAK TV. Archived from the original on 31 July 2019. Retrieved 31 July 2019.
  16. Television, Oak (30 July 2019). "Full Video: Senate confirms Buhari's 43 ministers". OAK TV. Archived from the original on 31 July 2019. Retrieved 31 July 2019.
  17. "FULL LIST: Buhari Assigns Portfolios To Ministers". Sahara Reporters. 2019-08-21. Retrieved 2019-08-22.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe

  Media related to Uchechukwu Sampson Ogah at Wikimedia Commons