Uche Chukwumerije
Uche Chukwumerije, (11 Janairu,1939 – 19 Afrilu, 2015), wanda aka fi sani da “Comrade Chukwumerije[1] ” saboda gwagwarmayar sa,[2] an zaɓe shi a matsayin Sanata a Tarayyar Najeriya a watan Afrilun,2003, mai wakiltar gundumar Abia ta Arewa.[1]
Uche Chukwumerije | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015 - Mao Ohuabunwa → District: Abia North
5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011 District: Abia North
3 ga Yuni, 2003 - 5 ga Yuni, 2007 ← Ike Nwachukwu District: Abia North | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Ogoja, 11 ga Janairu, 1939 | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Mutuwa | Abuja, 19 ga Afirilu, 2015 | ||||||
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (Ciwon huhun daji) | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta | Jami'ar Ibadan | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Imani | |||||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Chukwumerije a ranar 11 ga watan Janairun, 1939 a Ogoja,[3] a Jihar Kuros Riba ta Najeriya a yau, ga Sajan Ogbonna Chukwumerije (wanda aka fi sani da Sarji) da matarsa ta uku Mrs Egejuru Chukwumerije, dukkansu sun fito daga Isuochi a Jihar Abia ta Najeriya a yau. Shi ne na 4 a cikin ƴaƴan mahaifiyarsa su takwas: Daniel, Roland, Ahamefula (Joe), Ucheruaka, Ifeyinwa, Rosa, Ochi, Onyekozuoro (Onyex).
Ilimi
gyara sasheYa halarci Makarantar Methodist Central, Nkwoagu, Isuochi, Jihar Abia, 1943–52; Makarantar Sakandaren Uwargidanmu, Onitsha, 1953–57; Jami'ar Ibadan, 1958-61, inda ya karanci fannin tattalin arziki;[4] Faith Bible College, Sango-Ota, 1991-92.[5]
Farkon aiki
gyara sasheShugaban Features Desk, DailyTimes, 1961; Desk News, Nigerian Broadcasting Corporation (yanzu FRCN);
Fagen siyasa
gyara sasheChukwumerije ya yi ministan yaɗa labarai da al'adu a ƙarƙashin Janar Ibrahim Babangida[2] da kuma a ƙarƙashin gwamnatin wucin gadi ta ƙasa ta Ernest Shonekan.[3]
Majalisar Dattawa
gyara sasheA jamhuriya ta hudu, an zaɓi Chukwumerije a matsayin ɗan majalisar dattawa a tsarin jam’iyyar Peoples Democratic Party, amma ya kasa amincewa da shugabancin jam’iyyar a lokacin da ya ƙi amincewa da ajandar wa’adi na uku. Daga ƙarshe Chukwumerije ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Progressive Peoples Alliance a shekarar 2006, kuma aka sake zaɓen shi a majalisar dattawa a ranar 28 ga watan Afrilu, 2007.[5]
An sake zaɓen Chukwumerije a jam'iyyar PDP a zaɓen watan Afrilun 2011.[6]
Iyali
gyara sasheChukwumerije ya auri Gimbiya Gloria N. Iweka. Sun haifi 'ya'ya takwas:[7][8] Che Chidi (1974-), Kwame Ekwueme (1975-1995), Azuka Juachi (1976-), Dikeogu Egwuatu (1979-), Chaka Ikenna (1980-), Uchemruaka Obinna ( 1982-), da tagwayen Kelechi Udoka (1983-) da Chikadibia Yagazie (1983-). Chukwumerije da Gimbiya Iweka sun rabu a 1988. Daya daga cikin ƴa'ƴansu Chika ya samu lambar tagulla a gasar Olympics ta 2008 da aka yi a birnin Beijing.[6] Wani da, Dike, fitaccen marubucin Najeriya ne, mai magana da yawun jama'a kuma mawaƙin wasan kwaikwayo.[9]
Mutuwa
gyara sasheYa mutu a ofishi sakamakon ciwon huhu a shekara ta 2015.[10]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 Emmanuel, Ogala (2015-04-19). "How Senator Uche Chukwumerije died - Family - Premium Times Nigeria" (in Turanci). Retrieved 2020-01-22.
- ↑ 2.0 2.1 "RIOTING ERUPTS IN NIGERIA OVER CANCELLATION OF VOTE". Washington Post (in Turanci). ISSN 0190-8286. Retrieved 2021-03-10.
- ↑ 3.0 3.1 "Senator Chukwumerije dies of cancer - P.M. News" (in Turanci). Retrieved 2022-07-25.
- ↑ "Revealed: Senator Uche Chukwumerije – How He Passed On and Who He Was!". Nigerian Voice. Retrieved 2022-09-02.
- ↑ 5.0 5.1 Emmanuel, Ogala (2015-04-19). "How Senator Uche Chukwumerije died -- Family". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-07-25.
- ↑ 6.0 6.1 ORJI UZOR KALU (10 April 2011). "Orji Kalu Fails; Abaribe, Chukwumerije, Nwaogu Reelected Senators". Online Nigeria. Archived from the original on 28 July 2011. Retrieved 2011-04-20.
- ↑ vivianonuorah (2015-05-01). "MEET LATE SEN. UCHE CHUKWUMERIJE'S 7 KIDS". Vivys Archive (in Turanci). Retrieved 2022-09-03.
- ↑ Awa, Omiko (2011-12-28). "WELCOME TO OMIKO AWA'S BLOG: Chukwumerije… The Senator and his taekwondo clan". WELCOME TO OMIKO AWA'S BLOG. Retrieved 2022-09-03.
- ↑ "Dike Chukwumerije". THE GREEN INSTITUTE (in Turanci). Retrieved 2022-09-03.
- ↑ "Sen. Chukwumerije dies at 75" (in Turanci). Retrieved 2017-12-22.