Tony Okungbowa
Anthony Victor Okungbowa (an haife shi c.a shekara ta 1967 zuwa 1968)[1] ɗan wasan kwaikwayo ne Ba'amurke, mai shirya fina-finai, kuma DJ. Shi ne a matsayin DJ ga shiri wasan kwaikwayo mai dogon zango na The Ellen DeGeneres Show daga ashekara ta 2003 zuwa ta 2006 da kuma shekara ta 2008 zuwa ta 2013 lokacin da Stephen "tWitch" Boss ya maye gurbinsa. Ya dawo a matsayin bako a ranar 28 ga Afrilu, a shekara ta 2014. Tun daga shekara ta 2019, Okungbowa yadawo yana wasa a matsayin Kofo, a cikin sitcom na CBS Bob Hearts Abishola.
Tony Okungbowa | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Landan, 6 Disamba 1967 (56 shekaru) |
ƙasa | Tarayyar Amurka |
Harshen uwa | Turanci |
Karatu | |
Makaranta | Middlesex University (en) |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi, dan wasan kwaikwayon talabijin da disc jockey (en) |
IMDb | nm0645803 |
Rayuwar farko
gyara sasheOkungbowa dan Najeriya ne kuma ya girma a Najeriya da Landan.[2] Ya yi digiri a fannin wasan kwaikwayo daga Jami'ar Middlesex da ke Landan.[3] Ya koma Amurka a cikin shekara ta 1992, lokacin da ya zo yin digiri na biyu a gidan wasan kwaikwayo na Lee Strasberg da Cibiyar Fim a birnin New York, daga baya kuma, ya koma Los Angeles a shekara ta 1998.[1][3]
Sana'a
gyara sasheShirin The Ellen DeGeneres Show ya kunshi DJ don samar da kida, rawar da Okungbowa ya fara takawa a cikin shekara ta 2003 zuwa karshen zango na uku na wasan kwaikwayon a shekarar 2006, lokacin da ya tafi don haɓaka aikin wasan kwaikwayo.[4] Jon Abrahams ne ya maye gurbinsa a farkon shirin a zango na hudu. Ya dawo a shekara ta 2007 don musanyawa lokaci-lokaci, kuma ya koma cikakken DJ Mai samar da kida a lokaci gaba daya na zango na 6 na shirin wasan, wanda ya fara daga 8 ga watan Satumban, na cikin shekara ta 2008. Okungbowa kuma DJ's 2004 Grammy Awards.
Ayyukansa na irin rawar da yake takawa a fim sun hada da wuraren bako akan The X-Files, NYPD Blue, Doka & oda: Sashin Wadanda abin ya shafa na Musamman da NCIS: Los Angeles a cikin shekara ta 2014.
Ya kasance babban mai shiryawa kuma yayi aiki a cikin fim din Restless City wanda ya fara halarta a bikin Fim na Sundance acikin shekara ta 2011.[5]
A ranar 7 ga Janairu,acikin shekara ta 2013, Okungbowa ya zama dan Kasar Amurka.[6]
Fina-finai
gyara sasheFilm | |||
---|---|---|---|
Shekara | Fim | Matsayi | Bayani |
1993 | The Punk | Punk Friend #2 | |
2002 | The Wild Thornberrys Movie | Ranger | Voice |
2003 | Gate to Heaven | Amadou | |
2008 | Miracle of Phil | Seth | |
2009 | The One Last Time | Scarecow | |
2011 | Restless City | Bekay | |
CIS: Las Gidi | The Tax Man | ||
2013 | Mother of George | Biyi | |
2014 | Echo Park | Alex | |
Talabijin | |||
Shekara | Suna | Matsayi | Bayani |
1999 | The X-Files | Barnes' Driver | Episode: "The Sixth Extinction" |
2000 | Arli$$ | Homeless Joe | Episode: "Where There's a Will" |
2001 | NYPD Blue | Tristan L. Gibbs | Episode: "Fools Russian" |
2001; 2010 | The Bold and the Beautiful | Diver/Dempsey | 6 episodes |
2003–06; 2008–13 | The Ellen DeGeneres Show | Himself/DJ | 1,672 Episode |
2008 | Law & Order: Special Victims Unit | Dr. Bakari | Episode: "Trials" |
2014 | NCIS Los Angeles | Bakari Deng | Episode: "Exposure" |
2015 | Kids Say the Darndest Things Nigeria | Himself/host | 2 episode |
2017 | Ballers | Dr. Dester | Episode: "Alley-Oops" |
2017 | Ray Donovan | Bolaji | Episode: "Horses" |
2019–present | Bob Hearts Abishola | Kofo | Main role |
page:
Discography
gyara sasheMixed compilations
gyara sashe- 2005: Hollywood Sessions, Vol. 1
- 2009: Total Dance 2009
- 2012: "A Night to Remember"
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 King, Susan (January 8, 2006). "Putting his spin on TV talk". Los Angeles Times. Archived from the original on August 5, 2020.
Age: 38
Samfuri:Subscription - ↑ "Biography: Anthony Okungbowa"[permanent dead link], TV.com.
- ↑ 3.0 3.1 "Actor / DJ". Tony Okungbowa official website. Archived from the original on February 4, 2013..
- ↑ Kugel, Allison (June 1, 2006). "Tony Okungbowa: Resident Deejay on The Ellen DeGeneres Show Blazes His Own Trail in Hollywood" (Press release). Tony Okungbowa. Archived from the original on February 2, 2017 – via PR.com.
- ↑ Anderson, John (February 1, 2011). "Review: 'Restless City'". Variety.
- ↑ Tony is an American Citizen!. The Ellen DeGeneres Show. January 7, 2013. Archived from the original on 2021-12-17. Retrieved 2019-02-03 – via YouTube.