YouTube
YouTube kafar sadarwa ce da kuma dandalin watsa bidiyoyi ta yanar gizo ta Amurka wanda kamfanin Google ta mallake ta. Steve Chen, Chad Hurley, da kuma Jawed Karim ne suka ƙirƙiri Youtuba a ranar 14 ga Fabrairu, 2005, tsofaffin ma'aikatan Kamfanin PayPal. Hedikwata na San Bruno, California, Amurka, kuma a halin yanzu itace kafar yanar gizo na biyu da aka fi ziyarta, bayan Google Search. A cikin watan Junairun 2024, YouTube tana da masu amfani da ita fiye da biliyan 2.5 a kowane wata, waɗanda ke kallon sama da sa'o'i biliyan ɗaya na bidiyoyi a kowace rana.[1] Tun daga watan Mayun 2019, ana loda bidiyoyi aƙalla sama da sa'o'i 500 a duk bayan minti daya,[2][3] sannan kuma ya zuwa shekara ta 2023, akwai aƙalla bidiyoyi biliyan 14 gaba daya.[4]
YouTube | |
---|---|
| |
Broadcast Yourself | |
Bayanai | |
Gajeren suna | YT |
Iri | video streaming service (en) , online video platform (en) , user-generated content platform (en) , online community (en) da live streaming service (en) |
Masana'anta | Internet industry (en) da online video platform (en) |
Ƙasa | Tarayyar Amurka |
Aiki | |
Harshen amfani | multiple languages (en) |
Kayayyaki |
online video platform (en) , streaming media (en) , YouTube Kids (en) , YouTube Music (mul) , YouTube Premium (en) , YouTube Shorts (en) da YouTube TV (mul) |
Mulki | |
Hedkwata | San Bruno (en) |
Subdivisions |
YouTube channel (en) |
Mamallaki | YouTube (en) da Google |
Financial data | |
Haraji | 31,500,000,000 $ (2023) |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 14 ga Faburairu, 2005 |
Wanda ya samar | |
Awards received |
Peabody Awards (2008) |
|
Google ta siya Youtube a ranar 9 ga watan Oktoban 2006, akan kudi $1.65 (daidai da dala biliyan $2.31 a cikin shekara ta 2023),[5] Google ta fadada salon kasuwancin Youtube ta hanyar samar da kudin shiga don tallace-tallace, da samar da biyan kudi ga bidioyi kamar fina-finai da kuma masu kirkirar bidiyoyi na musamman a Youtube ko don saboda ita. Har wayau, tana samar da tsarin YouTube Premium, wani tsari na biya don kallo a Youtube ba tare da tallace-tallace ba. Youtube ta shigo da shirin Google's AdSense don samar da kudin shiga ga ita Youtube da kuma masu kirkira da aka yarje mawa. A cikin shekara ta 2023, kudin shiga na Youtube ya kai adadin dala biliyan $31.7, an samu karin kashi 2% daga $31.1 kamar yadda aka sanar a shekara ta 2022.[6] Daga ƙarshen watannin shekara ta 2023 zuwa tsakiyar watannin shekara ta 2024, adadin kudin shiga na Youtube daga tallace-tallace da kuma biyan kudi sun haura dala biliyan 50.[7]
Tun bayan da Google ta siye ta, Youtube ta fadada fiye da shafin yanar gizo zuwa app na waya, tashar telebijin, da kuma damar ta na hadaka da wasu kafofin. Nau'in bidiyoyi a Youtube sun hada da bidiyoyin waka, hotunan bidiyo, gajerun bidiyoyi, labarai, fina-finai, wakoki, labarun gaskiya, tallar fina-finai, tashar wasanni, kallo na kai tsaye, da dai sauran su. Mafi yawanci mutane ne ke kirkirar bidiyoyi a cikinta, wanda ya hada da hadaka a tsakanin 'Yan-Youtube da kuma masu daukan nauyinsu. Manyan kafofin midiya, labarai, da masana'antun nishadantarwa sun kirkira kuma sun karawa kawunansu shahara ta hanyar Youtube don riskar mutane da dama.
Youtube ta yi tasiri sosai a fannin zamantakewa, tayi tasiri akan fitattun al'adu, yayi na yanar gizo, kuma ta samar da shahararrun manyan masu kudi. Duk da nasarorinta, an soki kafar da assasa yaduwar ƙarerayi, da tauye haƙƙoƙin mallaka, cigaba da ƙetare sirrikan masu amfani da ita, tsauraran dokoki, da kuma sanya rayuwar yara acikin hatsari, da kuma rashin tsayayyen aiwatar da ƙa'idojin kafar.
Tarihi
gyara sasheƘirƙira da asalin haɓakar ta (2005–2006)
gyara sasheSteve Chen, Chad Hurley, da kuma Jawed Karim ne suka kirkiri YouTube. Su ukun da farko sun kasance ma'aikatan Kamfanin PayPal ne,[8] wanda hakan ya sa sun zamo masu kudi bayan eBay ta siya kamfanin. Hurley ya karanci design daga Jami'ar Indiyana ta Pennsylvania, sannan Chen da Karim sun karanci Kimiyyar Komfuta daga Jami'ar Illinois Urbana-Champaign.[9]
Dangane da wani labari da ake yawan fada a midiya, Hurley da Chen ne suka kirkiri dabarar Youtube a farkon shekara ta 2005, bayan sun sha wahalar watsa bidiyo da aka dauka a wajen fati na dina a gidan Chen a San Francisco. Karim bai halarci fatin ba kuma ya musunta faruwar hakan, amma kuma Chen ya bayyana cewa an kirkiri dabarar Youtube ne a wajen wani fati na dina ya kasance watakila dalilin da ya kara karfafawa 'yan kasuwa ra'ayin kirkirar labarin da za'a iya yarda da shi.[10]
Karim yace, dabarar Youtube ya zo ne daga Rikicin wasan hutun rabin sa'a na Super Bowl XXXVIII a yayin da Justin Timberlake ya ɗan bayyana nonon Janet Jackson a yayin hutun rabin sa'a. Karim ya sha wahalar gano bidiyon da kuma bidiyon ambaliyar ruwa a tekun Indiya na 2004 a yanar gizo, wanda ya janyo dabarar kirkiran shafin watsa bidiyoyi ta yanar gizo.[11][12] Hurley da Chen sun ce asalin dabarar Youtube ya zo ne daga wani nau'in bidiyo na shafin sada alaka ta yanar gizo kuma ya tasirantu daga wani shafin yanar gizo mai suna Hot or Not.[10][13] Suna turawa kyawawan mata sako a Craigslist suna ce musu su sanya bidiyoyinsu a shafin don samun kyautan dala $100.[14] Wahala don samun isassun bidiyoyin alaka ya janyo sauya dabara, inda wanda suka kirkiri shafin suka amince a rika daura kowanne irin bidiyo.[15]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Goodrow, Cristos (February 27, 2017). "You know what's cool? A billion hours" (in Turanci). Archived from the original on August 6, 2020. Retrieved April 19, 2021 – via YouTube.
- ↑ Loke Hale, James (May 7, 2019). "More Than 500 Hours Of Content Are Now Being Uploaded To YouTube Every Minute". TubeFilter. Los Angeles, CA. Archived from the original on January 5, 2023. Retrieved June 10, 2019.
- ↑ Neufeld, Dorothy (January 27, 2021). "The 50 Most Visited Websites in the World". Visual Capitalist (in Turanci). Archived from the original on December 10, 2021. Retrieved December 6, 2021.
- ↑ McGrady, Ryan (2024-01-26). "What We Discovered on 'Deep YouTube'". The Atlantic (in Turanci). Retrieved 2024-11-10.
- ↑ Hooker, Lucy (February 1, 2016). "How did Google become the world's most valuable company?". BBC News (in Turanci). Archived from the original on May 26, 2021. Retrieved May 26, 2021.
- ↑ "Alphabet Q1 2024 Earnings Release" (PDF). Alphabet Investor Relations. Retrieved November 1, 2024.
- ↑ "Google CFO Discusses YouTube's Advertising and Subscription Revenue". Business Insider. Retrieved November 1, 2024.
- ↑ Helft, Miguel; Richtel, Matt (October 10, 2006). "Venture Firm Shares a YouTube Jackpot". The New York Times. ProQuest 433418867. Archivedfrom the original on March 11, 2021. Retrieved March 26, 2017.
- ↑ "YouTube founders now superstars". The Sydney Morning Herald (in Turanci). October 11, 2006. Archived from the original on April 13, 2021. Retrieved March 18, 2021.
- ↑ 10.0 10.1 Cloud, John (December 25, 2006). "The YouTube Gurus". Time. Archived from the original on May 16, 2017. Retrieved March 26, 2017.
- ↑ Hopkins, Jim (October 11, 2006). "Surprise! There's a third YouTube co-founder". USA Today. Archived from the original on October 4, 2012. Retrieved March 26, 2017.
- ↑ McAlone, Nathan (October 2, 2015). "Here's how Janet Jackson's infamous 'nipplegate' inspired the creation of YouTube". Business Insider. Archived from the original on April 18, 2024. Retrieved April 13, 2024.
- ↑ Earliest surviving version of the YouTube website Wayback Machine, April 28, 2005. Retrieved June 19, 2013.
- ↑ "r p 2006: YouTube: From Concept to Hypergrowth – Jawed Karim". April 22, 2013. Archived from the original on December 21, 2021 – via YouTube.
- ↑ Dredge, Stuart (March 16, 2016). "YouTube was meant to be a video-dating website". The Guardian. Archived from the original on January 28, 2021. Retrieved March 15, 2019.