The Boy Kumasenu (fim)
The Boy Kumasenu wani fim ne da aka yi a shekarar 1952 a Ghana wanda wasu ’yan fim na Birtaniya suka yi. Sean Graham ne ya samar da shi gami da bada Umarni daga rubutun labarin na, Graham da John Wyllie. Kidan shirin fim din daga Elisabeth Lutyens. Fim ɗin ya shahara kuma ya yi tasiri ga zamantakewar jama'a. Ya nuna alamun abubuwan da za su iya nan gaba wanda ya sa ta zama alaƙa da adawa da mulkin mallaka da sauyin zamantakewa a sabuwar ƴancin kai na Ghana.[1]
The Boy Kumasenu (fim) | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 1952 |
Asalin harshe | Turanci |
Ƙasar asali | Ghana |
Characteristics | |
Genre (en) | drama film (en) |
During | 60 Dakika |
Launi | black-and-white (en) |
Direction and screenplay | |
Darekta | Sean Graham (en) |
External links | |
YouTube |
Shiryawa
gyara sasheThe Boy Kumasenu fim na farko da sashen fina-finai na Gold Coast ya yi, wanda ya nemi shirya fina-finai masu ilmantarwa da fadakarwa don rabawa a Ghana da kuma ƙasashen waje.[2] Daraktan shirin shine Sean Graham, wanda ya kasance ɗalibi ɗan jarida John Grierson, kodayake Graham ya fi son yin aiki da yawa a ɓangaren zantuntukan fitattun fina-finai. [2] Mawaƙi Guy Warren yana ɗaya daga cikin ƴan wasan kwaikwayo na shirin, wanda ke taka rawar gani a matsayin Yeboah.[3]
An yi fim ɗin a cikin 1950 da 1951 a Accra, Kedze da Keta, tare da jaruman shirin da ba ƙwararru ba, kuma an gyara fim din a birnin London. An ƙaddamar da shi a Ghana a shekarar 1952 amma masu yinsa sun sami matsala wajen rarraba shi a Ghana, saboda imanin cewa 'yan Afirka sun fi son fina-finai na tserewa. Koyaya, daga baya ya zama sananne sosai.[4][5] An ba shi takardar shaidar difloma ta Venice Film Festival kuma yana da farkonsa na Biritaniya a 1952 Edinburgh Film Festival ; An kuma nuna shi a bikin Fim na Berlin na 1953. [4] An zaɓi fim din don lambar yabo ta Fim ta Burtaniya don mafi kyawun fim a 1953.
An rarraba shi sosai a Burtaniya da Ghana. [2]
Makirci
gyara sasheFim ɗin ya ba da labarin wani yaro mai suna Kumasenu wanda ya yi ƙaura zuwa birnin Accra daga wani ƙaramin ƙauyen masu kamun kifi, wanda ɗan uwansa Agboh ya ƙara masa kwarin gwiwa game da abubuwan al'ajabi na rayuwar birni. Yana jin yunwa sai ya saci biredi sannan ‘yan sanda suka kama shi, amma likita da matarsa suka cece shi, suka same shi yana aiki. Agboh yayi ƙoƙarin ganin Kumasenu ya yiwa likitan fashi, amma Kumasenu ya dakile shirin dan uwansa.
Tsokaci
gyara sasheMujallar Variety ta yaba da shi a matsayin "kyakkyawan shirin fim" kuma sun ba da shawarar hakan na iya zama nasara a gidan fasaha. A ta bakin West African Review ta yi la'akari da cewa ya nuna wani muhimmin al'amari da ke fuskantar Afirka, kuma ya nuna ikon shugabancin Afirka na magance matsalolin Afirka. [4] Monthly Film Bulletin bai burge shi ba sosai, inda ya same shi "marasa hankali" duk da cewa yana yaba shi a matsayin mafari ga fina-finan Afirka. [4]
Nassoshi
gyara sashe- ↑ "The Boy Kumasenu". doi:10.1080/02533952.2013.852826. S2CID 145506083. Retrieved 2021-08-31. Cite journal requires
|journal=
(help) - ↑ 2.0 2.1 2.2 Diawara, Manthia (1992). African Cinema: Politics & Culture. Indiana University Press. p. 5.
The Boy Kumasenu.
- ↑ Kelley, Robin D. G. (2012). Africa Speaks, America Answers: Modern Jazz in Revolutionary Times. Harvard University Press. p. 11.
- ↑ 4.0 4.1 4.2 4.3 Cite error: Invalid
<ref>
tag; no text was provided for refs namedcf
- ↑ Essah, Doris S. (2008). Fashioning the Nation: Hairdressing, Professionalism and the Performance of Gender in Ghana, 1900--2006. p. 74. ISBN 9780549840329.[permanent dead link]
Karin Karatu
gyara sasheBloom, Peter; Kate Skinner (2009–2010). "Modernity and Danger: The Boy Kumasenu and the Work of the Gold Coast Film Unit" (PDF). Ghana Studies. 12-13: 121–153. doi:10.1353/ghs.2009.0006.
Hanyoyin Hadi na waje
gyara sashe- "The Boy Kumasenu (1952)" at IMDb