Bajoga2021
Barka da zuwa!
gyara sasheBarka da zuwa Hausa Wikipedia, Bajoga2021! Mun ji daɗin gudummuwarku. Kuma ina fatan zaku tsaya ku ci gaba da bada gudummuwa. Anan ƙasa ga wasu shafuka da zasu taimaka wajen fahimtar Hausa Wikipedia da yadda ake gyara ta:
- Gabatarwa
- Tutorial
- Cheatsheet
- Yadda ake rubuta muƙala
- Manufofin Hausa Wikipedia
- Shawarwari goma akan gyaran Wikipedia
Zaku iya yin sayinin rubutunku idan kuna akan shafukan tattaunawa ta hanyar alamar tilde guda huɗu, kamar haka (~~~~); yin hakan, zaisa sunanku da cikkaken kwanan wata. In kana buƙatar wani taimako, ku duba Wikipedia:Tutorial, ko kuma ka tambayeni a . Na gode.Em-mustapha talk 16:34, 13 ga Yuni, 2022 (UTC)
Jan-hankali
gyara sasheAssalam, Barka da ƙoƙari, ina son jan hankalin ka game da sabuwar maƙala da ka ƙirƙira akan Julius Momo Udochi, akwai ƙura -kurai acikin fassarar amma kaɗan ne kayi ƙoƙari ka gyara, sai dai nan gaba kayi ƙoƙarin yin rubutu mai inganci ba tare da kuskure ba! Yin maƙala mara kyau na haifar kawo lahani sosai da ka iya ɓata sunan Wikipedia. Dafatan za'a gyara, Nagode
- Barka da ƙoƙari, ina son in ƙara jan hankalin ka game da wannan maƙala Tarihin_Jamhuriyar_Nijar bata da fassara mai kyau kuma akwai tarin kurakurai aciki sosai, dan sai da na duba asalin shafin dake a Wikipedia ta Turanci. Gaskiya za'a goge ta, kuma ina baka shawara duk shafin da ka san cewa baka da ƙwarewa a fannin sosai, to ba dole ne sai ka sa kanka fassara ta ba, ka bari wani zai zo da yake da ƙwarewa a wannan fannin sai yayi! Sannan ka bibiyi shafukan da ka ƙirƙira dan gyara su, saboda har yanzu wasun su na buƙatar gyara sosai. Pages created by Bajoga2021 Mungode Em-mustapha talk 11:57, 17 ga Janairu, 2023 (UTC)
Ka diba email naka.
gyara sasheAslm barka @Bajoga2021, na tura maka saƙo ta Email ina fata zaka diba. BnHamid (talk) 17:28, 18 ga Maris, 2023 (UTC)
Game da reference
gyara sasheAslm @Bajoga2021, muna matukar jinjina maka da gudummawar da kake bada wa a wannan shafi namu na Hausa Wikipedia. Naga kana sanya link a matsayin manazarta/reference. Idan zaka saka link sai dai jero su acikin Hanyoyin hadin waje wato External links. Idan kuwa kana so zaka iya bude shafi ta turanci kayi generating link din ya baka reference sai ka kwafo ka daura. Da fatan ka gane. Nagode.Patroller>> 15:32, 10 ga Afirilu, 2023 (UTC)
- Wslm@Uncle Bash007, na fahimci gyaran da kake ƙoƙarin nuna Mani kuma na fahimta in sha Allah za'a gyara. Nagode>>Bajoga2021 (talk) 15:45, 10 ga Afirilu, 2023 (UTC)
- Madallah.. Allah kara yi mana jagora baki daya.. keep it up.~~~ Patroller>> 17:17, 10 ga Afirilu, 2023 (UTC)
Jan Hankali
gyara sasheAslm alaikum@Bajoga2021, Barka da kokari...naga ka fassara mukalar Robert Eziakor, amma baka saka mata madogara koda dayaba...yakamata mu ringa inganta ayyukanmu da manazarta, NagodeSaifullahi AS (talk) 07:20, 15 Oktoba 2023 (UTC)