Tattalin arzikin duniya
Abu ne sananne kuma a hukumance cewa, rikicin tattalin arzikin Amirka ya zama ruwan dare gama duniya. To amma duk da haka wasu ƙasashen sun fi wasu taɓuwa idan ana batun matsayin irin illar da rikicin yai wa ƙasashen duniya. Wato ma'ana idan Amurka abin ya shafeta 100 bisa 100, to su ƙasashen da rikicin yai wa sauƙin taɓawa, abin bai wuce da kashi 1 zuwa 20 bisa dari ya shafe su ba.
Tattalin arzikin duniya | |
---|---|
type of crisis (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | economic crisis (en) , financial risk (en) da social crisis (en) |
Ƙasa ta farko da ba ta jin wannan rikici na tattalin arzki a jikinta, ita ce Tarayyar Daular Larabawa, wato "United Arab Emirates:". Duk da cewa tana da matsalar cikin gida na batun hallata kuɗin haram, amma dai duk da haka arzikin ƙasar yana ci gaba da haɓaka, kamar ma ba su san da wani rikicin tattalin arzikin duniya ba.
Ƙasar ta biyu ita ce ƙasar Armeniya. Itama duk da cewa tana da rikicinta na cikin gida ta ɓangaren rashin yin cuɗanya da kasuwannin duniya, don haka tana buƙatar bunƙasa shirinta na kasuwanci tsakanin ƙasa da ƙasa. To sai dai kuma labari mai daɗin shi ne, rashin yin wani ƙasaitaccen kasuwanci na ƙasa da ƙasa ya kare ta daga faɗawa dumu-dumu cikin rikicin tattalin arzikin na duniya ta tsinci kanta. Kai wasu ma na ganin cewa, ita ya kamata ta zamo ta farko a cikin ƙasashen da wannan rikicin na tattali bai shafa ba?
Ƙasa ta uku da rikicin tattalin arziki bai shafa sosai ba ita ce Maroko. Ko dadai ita Maroko ta yi dumu-dumu wajen harkokin cinikayya tsakanin ƙasa da ƙasa, musamman ma dai da ƙasar Faransa, da kuma batun harkokin yawon buɗe ido, waɗanda ake ganin waɗannan hanyoyi guda biyu suna samun tawaya saboda rikicin tattalin arzkin da Amirka ta jazawa duniya. To sai dai kuma labari mai daɗin shi ne, ma'adanan ƙarƙashin ƙasa da Allah ya huwace wa ƙasar, sun isa su ba ta ikon maye gurbin duk wani abu da za ta iya rasawa sakamkon rikicin tattalin arzikin.
Bildunterschrift: Großansicht des Bildes mit der Bildunterschrift: Dogwayen gine-ginen birnin Kuala Lumpur a Malesiya Kasa ta huɗu a duniya wajen rashin jin raɗaɗin rikicin tattalin arziki ita ce ƙasar Malesiya. Duk da cewa Malesiya ta kai iya wuya wajen yin hulɗar cinikayya da Amirka, to amma abin daɗin shi ne, kamfanonin Amirkan da suke buƙatar rage yawan kuɗaɗen da suke kashewa, yanzu haka ƙasar Malesiyan suke komawa suna sarrafa kayayyakinsu a can, saboda sauƙin biyan ma'aikata.
Ƙasa ta biyar kuwa ita ce Iran. kuma ya ɗan shafe ta ne saboda hulɗar kasuwancin da take yi da ƙasashen Turai, duk da cewa tana yin hakan ne a ƙarkashin takunkumi. To amma labari mai daɗi ga Iran shi ne cewa, ba ta yin hulɗar kasuwanci da Amirka, ƙasar da ta haddasa rikincin tattalin arzikin. Sannan tana daga cikin ƙasashen da suke sayar da mai ga ƙasar chaina, wanda ake ganin ko wannan ciniki na mai da chaina kaɗai ya isa ya riƙe ƙasar Iran tsawon shekaru goma.
Ƙasa ta shida it ace ƙasar Koriya ta Arewa: Labari mara daɗi a gare ta shi ne, babu baki masu sanya jari a cikin harkokin noma da bunƙasa samuwar abinci a wannan kasa, to amma kuma ware tan da aka yi ba a hulɗar ciniki da ita sosai, ya sanya matsalar tattalin arziki ta sa me daidai ruwa daidai tsaki.
Ƙasa ta bakwai kuwa ita ce, ƙasar Tailan. Kuma abin ma da ya sa rikicin ya shafe ta shi ne, kasancewar babban kamfanin da ke gudanar da harkokinsa a ƙasar wani reshe ne na kamfanin inshorar nan na Amirka AIG, wanda rikicin tattlin arzikin Amirka ya fara rutsawa da shi. To amma labari mai daɗin shi ne, ƙasar ta dogara ne da amfani da tsaɓar kuɗi da kuma ciniki na ƙeƙe-da ƙeƙe wajen harkokin kasuwanci.
Daga ƙasar Tailan sai Romaniya. rikicin ya ɗan shafi Romaniya ne, saboda yadda ta ɗan yi zurfi wajen cinikayya da tarayyar Turai da kuma yadda take ciniki kai tsaye da sauran ƙasashen waje. To sai dai abin farin ciki ga ƙasar shi ne, har yanzu tana nan a matsayin ƙasar da kamfanonin nahiyar Turai suka ɗauka a matsayin wani sansani na hada-hadarsu.
To ƙasa ta tara ita ce ƙasar Brazil. Kuma rashin sa'ar da tai shi ne cewar, ƙasar Amirka ita ce babbar abokiyar cinikinta. To amma kuma labari mai daɗi ga ƙasar shi ne na kasancewarta a wani matsayi na samun yarjejeniyar kasuwanci na ƙasa da ƙasa tsakanin ta da ƙasar Indiya da Chaina. Wanda waɗannan ƙasashe biyu yanzu haka suna matsayi na ƙoli-ƙoli a haɓakar tattalin arziki a duniya.
Bildunterschrift: Großansicht des Bildes mit der Bildunterschrift: Takardar kuɗin Chaina ta Yuan 100Ƙasa ta goma kuwa a jerin ƙasashen da raɗaɗin rikicin tattalin arziki ya taɓa da sauƙi-sauƙi ita ce ƙasar Chaina. Kuma illar da wannan rikici yai mata shi ne, na yadda ƙasar Amirka da ƙasashen nahiyar Turai sukai tsananin rage buƙatar kayayyaki daga gare ta. Kuma har yanzu hakan na ci gaba da yin tasiri akan tattalin arzikinta. To amma kasancewar Chaina a matsayin ƙasa mafi yawan al'umma a duniya, hakan ya sa tattalin arzikin yana jure rikicin, saboda dogaro da take da shi akan kayayyakin da al'ummar ƙasar ke buƙata da kuma sauran ƙasashen da rikicin bai taba su sosai ba, irin su Brazil. Sannan kuma har ila yau Chaina na dogaro da irin tsabar kuɗin da take bin amirka bashi, musamman ma dai ta fuskar rancen da take bayarwa domin ceto masana'antun Amirkan da ga rugujewa.