Shantu wani abu ne dangin kwarya,tsawonsa kamar tsawon hannu daga yatsu zuwa kafada sai dai bai kai kaurin hannu ba ana yanke kowa ne karshen nasa, a rarake cikin sa kamar dai Dan guntun fayil na ruwa.mata na amfani dashi wajen rera wakoki suna bugashi akan ciya su Kuma Rika kada shi da Yan yatsu.