Sunday Paul Bako

malami a Najeriya

Sunday Paul Bako (an haife shi a ranar 10 ga Maris 1962) malami ne a Najeriya, mai bincike, kuma shugaban Jami'ar Jihar Taraba na uku, Jalingo.[1][2]

Sunday Paul Bako
Rayuwa
Haihuwa Takum da Jahar Taraba, 1962 (61/62 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a Malami da mataimakin shugaban jami'a
Employers Jami'ar Ahmadu Bello  (2006 -
Jami'ar Jahar Taraba  (1 ga Maris, 2022 -

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Sunday a garin Takum, Jihar Taraba, ranar 10 ga Maris, 1962.[1] Ya yi digirinsa na farko, B.Sc. (Botany) a shekara ta 1986, digiri na biyu, M.Sc. a shekara ta 1990, da digiri na uku, Ph.D. (Plant Eco Physiology) a shekara ta 2000 a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.[1]

Sunday Paul Bako ya fara aikinsa a matsayin Graduate Assistant a shekara ta 1987 a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. A shekarar 2006, an kara masa girma zuwa mukamin Farfesa. Kafin a nada shi a matsayin shugaban Jami’ar Jihar Taraba, Jalingo, ya kasance Shugaban Jami’ar Kwararafa dake Wukari.[1]

Aikin gudanarwa

gyara sashe

Sunday ya fara aikin gudanarwa ne a lokacin da yake Shugaban Jami’ar Kwararafa, Wukari kafin a nada shi a ranar 1 ga Maris, 2022 a matsayin Shugaban Jami’ar Jihar Taraba.[1]

Shi memba ne na Botanical Society of Nigeria (BOSON) da kuma Ecological Society of Nigeria (EcoSON).[1]

Karramawa

gyara sashe

A shekara ta 2018, Rotaract Club District 9125 ne ta ba shi lamabar yabo a matsayin Mafi Kwazon Shugaban Jami’a na Shekarar.[1]

Wallafe-Wallafe

gyara sashe

Sunday a matsayin shin a mai bincike, ya ba da gudummawa ga duniyar ilimi tare da littattafai sama da 120;[1] wasu daga cikin waɗannan su ne:

  • Effects of Plant Age, Ascorbate and Kinetin Applications on Nitrate Reductase Activity and Leaf Protein Content of Maize (Zea mays L.) Plants Grown under Heat Stress[3]
  • Occurrence and Distribution of Aquatic Macrophytes in Relation to the Nutrient Content in Sediments of Two Freshwater Lake Ecosystems in the Nigerian Savanna[4]
  • Trace Metal Contents of the Emergent Macrophytes Polygonum sp.and Ludwigia sp. In Relation to the Sediments of Two Freshwater Lake Ecosystems in the Nigerian Savanna[5]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 1.6 1.7 "Prof. Sunday Bako – Vice-Chancellor | Taraba State University" (in Turanci). Retrieved 2024-09-14.
  2. Editor (2023-08-12). "Taraba State University bans prohibited wears". Champion Newspapers LTD (in Turanci). Archived from the original on 2024-09-14. Retrieved 2024-09-14.CS1 maint: extra text: authors list (link)
  3. "Effects of Plant Age, Ascorbate and Kinetin Applications on Nitrate Reductase Activity and Leaf Protein Content of Maize (Zea mays L.) Plants Grown under Heat Stress". scialert.net (in Turanci). Retrieved 2024-09-14.
  4. "Occurrence and Distribution of Aquatic Macrophytes in Relation to the Nutrient Content in Sediments of Two Freshwater Lake Ecosystems in the Nigerian Savanna". scialert.net (in Turanci). Retrieved 2024-09-14.
  5. "Trace Metal Contents of the Emergent Macrophytes Polygonum sp.and Ludwigia sp. In Relation to the Sediments of Two Freshwater Lake Ecosystems in the Nigerian Savanna". scialert.net (in Turanci). Retrieved 2024-09-14.