Sidi Ahmed Rguibi

Mai wa'azin addinin Musulunci daga Sahrawi kuma shugaban Siyasa

Sidi Ahmed Rguibi ( Larabci: سيدي أحمد الركيبي‎ ) ya kasance Balarabe mai wa'azin addinin Islama ko Musulunci na Sahrawi kuma jagoran siyasa daga ƙabilar Beni Hassan, a yankunan kabilanci na hamadar arewa maso yammacin Sahara a ƙarni na 16. An haife shi a shekarar 1590 a El Kharaouiaa. An dauke shi a matsayin mutum mai tsarki kuma idrissid, ko zuriyar Muhammadu. Ya rasu yana da shekaru 75 a duniya.[1][2][3]

Sidi Ahmed Rguibi
Rayuwa
Haihuwa 1590
Mutuwa 1665
Sana'a
Sana'a Mai da'awa da ɗan siyasa
Muhimman ayyuka Reguibat tribe (en) Fassara
Imani
Addini Mabiya Sunnah

Shi ne wanda ya kafa Reguibat, ƙabilar Sahrawi mafi girma kuma mafi ƙarfi, waɗanda yankunansu suka tashi daga yammacin Sahara zuwa inda a yau a nan ne kasashen Mauritaniya, Maroko da Aljeriya.

Dubban maziyarta ne ke ziyartan wurin ibadarsa, dake arewacin Saguia el Hamra na yammacin Sahara a kowace shekara.

Manazarta

gyara sashe
  1. Bahi, Mohamed Ahmed (1998). الليث سيدي أحمد الركيبي [the Lion, Sidi Ahmed Rguibi] (in Larabci). Kenitra: Editions Boukili.
  2. Caratini, Sophie; Monod, Théodore (1989). "Des chameliers à la conquête d'un territoire". Les Rgaybat (1610-1934) (in Faransanci). Paris: l'Harmattan.
  3. Caratini, Sophie; Meillassoux, Claude (1989). "Territoire et Société". Les Rgaybat (1610-1934) (in Faransanci). Paris: l'Harmattan.