Shehu Dikko
Shehu Dikko (an haife shi a Kaduna, Nijeriya ) shi ne mai kula da harkokin ƙwallon ƙafa a Nijeriya]. Shi ne Shugaban Kamfanin Gudanar da Kungiyar wanda ke da alhakin kula da Kungiyar Kwallan Kafa ta Najeriya.Ya taba zama mai ba da shawara ga majalisar wakilan Najeriya kan kwamitin wasanni.[1][2] .[3][4][5].
Shehu Dikko | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | Jihar Kaduna, | ||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | association football manager (en) | ||||||||||||||||||
|
Rayuwar mutum da ilimi
gyara sasheAn haifi Dikko a jihar Kaduna, Najeriya . Ya halarci jami'ar Ahmadu Bello inda ya karanci Quantity Surveying kuma ya kammala a BSc. Ya kuma yi difloma a fannin gudanarwa daga wannan jami'ar. Bayan haka ya sami digirinsa na biyu na harkokin kasuwanci daga Jami'ar Ahmadu Bello .
Ayyuka
gyara sasheShehu Dikko ya kasance kafin shiga harkar kwallon kafan kwararru yana aiki a kamfanoni masu zaman kansu tsakanin shekara ta alif1991 da shekara ta dubu biyu da goma Sha hudu 2004. A shekara ta 2004, lokacin da ya shiga harkar kwallon kafa a Najeriya ya fara a matsayin FIFA Goal Project Manager na najeriya tare da shirya yawon shakatawa da yawa tsakanin Portsmouth FC da Manchester United tare da Kano Pillars FC.A shekara ta 2008, an dauki Shehu Dikko matsayin mai ba da shawara ga kwamitin wasanni a Majalisar Wakilan Najeriya inda ya yi aiki har zuwa 2011.Yayin da yake mai ba gwamnati shawara,ya taimaka wajen tsara dokar Hukumar Wasanni ta Kasa a Majalisar Dokoki ta Kasa . A shekara ta 2012 aka nada shi sakataren kungiyar Super Eagles Bonus Row da kuma ka'idojin tsara ayyuka har zuwa shekara ta 2013.A watan Satumbar shekara ta 2014,ya yi takarar shugabancin NFF amma ya janye takararsa kafin a gudanar da zabe a hukumance.
A ranar 26 ga Disamban shekara ta 2014,an nada shi Shugaban Kamfanin Gudanar da League na Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya.[6][7][8][9][10][11][12][13][14][15] A ranar 4 ga Afrilun shekara ta 2019 an sake nada Shehu Dikko a matsayin Shugaban Kamfanin Gudanar da Kungiyar.
Umurnin kotu
gyara sasheA ranar goma Sha tara 19 ga Afrilun shekara ta dubu biyu da goma Sha shida. 2016,Dikko ya ba da umarnin dakatar da Giwa FC bayan da kungiyar ta karya dokokin NPFL da dama daga cikin tuhumar akwai kuma cin zarafin alkalin wasa da sauran jami’ai yayin wasa.Bayan dakatarwar,kungiyar Giwa FC ta maka LMC da Shehu Dikko kara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke jihar Filato.A ranar 16 ga watan Agustan shekara ta 2016 kotu ta umarci Shehu Dikko da ya maida Giwa FC cikin NPFL.
A watan Satumbar shekara ta 2016, wata babbar kotun tarayya da ke Jos ta ba da umarnin a kamo Dikko saboda rashin dawo da Giwa FC Daga baya an nemi ya bayyana a gaban kotun kuma lokacin da ya ki bayyana a kotun,kotun ta yanke hukuncin daurin makonni biyu ga Shehu Dikko.[16][17].
Manazarta
gyara sashe- ↑ Ahmadu, Samuel. "Football can grow the Nigerian economy – LMC boss Shehu Dikko | Goal.com". www.goal.com (in Turanci). Retrieved 2019-04-30.
- ↑ Inyang, Ifreke (2014-12-28). "Shehu Dikko appointed new League Management Company boss". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2019-04-30.
- ↑ Inyang, Ifreke (2015-12-03). "NPFL, 22 other leagues form World Leagues Association in France". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2019-04-30.
- ↑ Adeyanju, Kola (2019-04-29). "The LMC / La Liga U 15 will be a continuous events . Shehu Dikko". Latest football news in Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 2019-04-30. Retrieved 2019-04-30.
- ↑ editor (2019-04-30). "Dikko, Adepoju Count Gains of NPFL/LaLiga U-15 Tournament". THISDAYLIVE (in Turanci). Retrieved 2019-04-30.CS1 maint: extra text: authors list (link)
- ↑ "FCT INFRASTRUCTURAL DEVELOPMENT: ENGINEERING WORK ON KATAMPE DISTRICT SATISFACTORY". aitonline.tv (in Turanci). Retrieved 2019-04-30.[permanent dead link]
- ↑ Legit.ng (2013-08-20). "N5.4bn Broadcast Deal For Nigerian League". Legit.ng – Nigeria news. (in Turanci). Retrieved 2019-04-30.
- ↑ "League Management Company has the backing of the Nigerian Government". KickOff. Archived from the original on 2019-04-30. Retrieved 2019-04-30.
- ↑ "Governor Uduaghan Accused Of Bribing Football Federation Voters To Select His Wife's Brother As President". Sahara Reporters. 2014-10-02. Retrieved 2019-04-30.
- ↑ "NFF presidential election: The 5 men and their mission". TheCable (in Turanci). 2014-09-24. Retrieved 2019-04-30.
- ↑ "Governor Uduaghan Accused Of Bribing Football Federation Voters To Select His Wife's Brother As President". Sahara Reporters. 2014-10-02. Retrieved 2019-04-30.
- ↑ "Pinnick elected Nigeria Football Federation president" (in Turanci). 2014-09-30. Retrieved 2019-04-30.
- ↑ Ahmadu, Samuel. "Shehu Dikko is new League Management Company boss | Goal.com". www.goal.com (in Turanci). Retrieved 2019-04-30.
- ↑ "LMC reappoints Dikko as chairman, Irabor, others independent directors". guardian.ng. Archived from the original on 2019-04-30. Retrieved 2019-04-30.
- ↑ editor (2019-04-04). "LMC's EGM Reappoints Dikko, Independent Directors". THISDAYLIVE (in Turanci). Retrieved 2019-04-30.CS1 maint: extra text: authors list (link)
- ↑ Inyang, Ifreke (2016-09-22). "LMC chairman, Shehu Dikko declared wanted". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2019-04-30.
- ↑ adekunle (2016-09-21). "Dikko declared wanted!". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2019-04-30.