Shah ( Persian ) kalma ce ta Fasha wacce ke nufin sarki ko mai mulkin wata ƙasa. Ana amfani da wannan kalmar a ƙasashe daban-daban na duniya, ciki har da Iran, Indiya, Pakistan da Afghanistan . A halin yanzu ana amfani da kalmar "Shah" a matsayin sunan uba ga yawancin mutane a Indiya, Pakistan da Afghanistan waɗanda suke Hindu, Musulmai da Jain. Sunaye da yawa na Indiya waɗanda ke da Shah a cikinsu; sanannen cikinsu shi ne Shah Jahan, wanda a matsayinsa na Sarkin Indiya ya ba da umarnin ƙirƙirar Taj Mahal . Aya daga cikin mahimman kalmomin da ake amfani da su a cikin chess shine matanin shah na Persia, ma'ana "sarki ba zai iya tserewa ba" [1]

Shah
noble title (en) Fassara da historical position (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na ruler (en) Fassara da Sultan (en) Fassara
Ƙasa Safavid Empire (en) Fassara

Kalmar "Shah" galibi tana nufin Mohammad Reza Pahlavi, Shah na Iran daga 1949 zuwa 1979.

Manazarta gyara sashe

  1. Definition and origins of Checkmate