Saud ibn Ibrahim ibn Muhammad al-Shuraim (Larabci: سعود بن ابراهيم بن محمد الشريم،, an haife shi a ranar 19 ga watan January shekara ta, alif dubu daya da dari tara da sittin da shida (1966[1]) yana daga cikin limamai da khateeb na babban masallacin Harami (Masjid al-Haram) dake Makkah. Sananne kuma shahararren makarancin alkur'ani wato qari, yanada digirin digirgir wato digiri na uku Dakta da turanci Doctor of Philosophy|doctorate (PHD) kuma farfesa ne a fannin Sharia da karatun addinin Musulunci a Jami'ar Umm al-Qura a Makkah. An zabi Shuraim amatsayin Dean da kuma "Kwararren Farfesa a fikihu (Fiqh) duk a jami'ar.[2]

Saud Al-Shuraim
Rayuwa
Cikakken suna سعود بن إبراهيم بن محمد بن إبراهيم آل شريم
Haihuwa Riyadh, 19 ga Janairu, 1966 (58 shekaru)
ƙasa Saudi Arebiya
Harshen uwa Larabci
Karatu
Makaranta Jami'ar Imam Muhammad ibn Saud Islamic
Umm al-Qura University (en) Fassara
Harsuna Larabci
Malamai Muhammad Yahya Rasool Nagari (en) Fassara
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a mai shari'a da Liman
Imani
Addini Musulunci

Ansansa a matsayin maibincike a Fikihu. Mai shari'a ne kuma marubuci wanda yayi rubuce rubuce da dama a fannin Aqidah, filihu, da Arabic poetry. Kuma yana daga cikin manyan malaman kasar Saudiya.

Shuraim yana jagorancin sallar Taraweeh a lokutan Ramadan a Mecca, yafara tun daga shekara ta, alif 1991. Kuma yana gudanar da sallar jana'iza (Sallar mamaci) wa tsohon yarima marigayi Nayef bin Abdulaziz a ranar 17 ga watan June shekara ta, 2012 bayan Maghrib (faduwar rana) a masallacin Harami.[3] Sarki Abdullah na Saudiya da yan Gidan sarautar kasar sun halarta jana'izar. Muryar sa lokacin karatu, yayadu a duniya ta fannoni daban-daban.

Manazarta

gyara sashe
  1. http://www.assabile.com/saud-shuraim-11/saud-shuraim.htm
  2. http://www.assabile.com/saud-shuraim-11/saud-shuraim.htm
  3. "Archived copy". Archived from the original on September 25, 2015. Retrieved July 1, 2016. Unknown parameter |deadurl= ignored (|url-status= suggested) (help)CS1 maint: archived copy as title (link)