Victoria (Alexandrina Victoria; ta rayi daga 24 ga Mayu 1819 - 22 ga Janairu 1901) ta kasance Sarauniyace ta Ƙasar Ingila ta Burtaniya da Ireland daga 20 ga Yuni 1837 har zuwa mutuwarta a shekarar 1901.
Tayi Sarautarta a shekaru 63 da kwanaki 216 - wanda ya fi na kowane magabata - da yayi Zamanin Victorian. Lokaci ne na canjin masana'antu, siyasa, kimiyya, da soja a cikin Ƙasar Ingila, kuma an nuna shi da babban fadada Daular Burtaniya.
A shekara ta 1876, Majalisar dokokin Burtaniya ta kada kuri'a don ba ta ƙarin taken Empress of India .