Saratu Mahmud Aliyu Shinkafi

Matar Gwamna

Saratu Mahmud Aliyu Shinkafi ta kasance uwargidan gwamnan jihar Zamfara a shekara ta 2007 a matsayin matar ga Gwamnan jihar Zamfara na biyu, Alhaji Mahmud Aliyu Shinkafi. Ita ce ta kafa kuma ta fara shirin Smart Initiative of Women Empowerment Foundation.[1]

Saratu Mahmud Aliyu Shinkafi
Rayuwa
Haihuwa Shinkafi
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Abokiyar zama Mahmud Shinkafi
Sana'a

Kuruciya da Ilimi gyara sashe

An haifi Hajiya Saratu a garin Shinkafi, ga dangin Alhaji Nuhu shinkafi da Balkisu Nuhu Shinkafi kimanin shekara 38 da suka shude. Ta fara karatunta ne da zuwa makarantar Qur’ani tun tana da shekara uku a duniya. Daga nan ne aka rubuta mata takardar zuwa Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Technical) da ke Gusau, inda ta nemi takardar shaidar NCE.

Aiki gyara sashe

Hajiya Saratu Aliyu ta kasance mata ga tshohon gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Mahmud Aliyu Shinkafi. Ta kasance jagorar Cibiyar Ilimi na Mata, kuma babban mai bada shawara ta musamman ga Gwamna Shinkafi akan harkokin da suka shafi mata da kananan yara a jihar. Har wayau ta kasance wacce ta samar da gidauniyar Smart Initiative of Women Empowerment Foundation.

Rayuwa gyara sashe

Hajiya Saratu sunyi aure da Alhaji Mahmud Aliyu Shinkafi kuma ya zama gwamna na biyu a jihar Zamfara a ranar 14 ga watan Afrilun shekara ta 2007.[2] Suna da 'ya'ya tare.

Littafi gyara sashe

  • Kabir, Hajara Muhammad. Ci gaban matan Arewa. [Nijeriya]. ISBN 978-978-906-469-4 . Saukewa: OCLC890820657.

Manazarta gyara sashe

  1. Kabir, Hajara Muhammad (2010). Northern women development. Nigeria. p. 183. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.
  2. "Mamuda Aliyu Shinkafi". Combster.tv. Retrieved 2022-06-07.