A cikin Sufanci, Salatul Fatih (Larabci: صَلَاةُ الْفَاتِحِ‎, "Sallar budewa") litany ce ta yau da kullun (wird) da kuma addu'a ga Muhammad daidaiku ko a cikin jama'a mabiya (murids) a cikin darikar Tijjaniyya.[1][2]

Salatul Fatih
littafi
Bayanai
Harshen aiki ko suna Larabci


Gabatarwa

gyara sashe

Salat al-Fatih da aka fi sani da Durood Fatih a cikin yankin Indiya da Sholawat Fatih a Gabashin Asiya mai Nisa.[3]

Sheikh Muhammad bn Abi al-Hasan al-Bakri daga zuriyar Abu Bakr al-Siddiq ne ya watsa wannan litattafai ga musulmi.[4]

Ana kuma danganta ta ga Sheikh Ahmad al-Tijjani wanda yakasance jikan Annabi Muhammad (S.A.W)https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.scribd.com/document/534138666/TARIHIN-SHEHU-TIJJANI&ved=2ahUKEwj40YLT_tiEAxXGUEEAHZ1cDmEQFnoECBkQAQ&usg=AOvVaw0xECLckY2g5bdPkH2hJNC_, shine kuma ya assasa darikar tijjaniyya, kuma a hakikanin gaskiya miliyoyin darikar tijjaniyya ne suke karanta wannan addu'a a duk fadin duniya a matsayin wani bangare na tsarinsu na yau da kullum.[5]


Cikakken rubutu da ingantaccen tsarin wannan littatafan da addu'a ga Muhammad shi ne kamar haka:[6]

لَّهُمَّ صَلِّ عَلَى سَيِّدِنَا مُحَمَّدِ الْفَاتِحِ لِمَا أُغْلِقَ، وَالْخَاتِمِ لِمَا سَبَقَ، نَاصِرِ الْحَقِّ بِالْحَقِّ، الْهَادِي إِلَى صِرَاطِكَ الْمُسْتَقِيمِ، وَعَلَى آلِهِ حَقَّ قَدْرِهِ وَمِقْدَارِهِ الْعَظِيمِ.

Hausa: Ya Allah ka yi salati ga shugabanmu Muhammadu, mabudin abin da aka rufa, da hatimin abin da ya gabata, mai taimakon gaskiya da gaskiya, kuma mai shiryarwa zuwa ga tafarkinka madaidaiciya. Allah ya yi salati ga Iyalan gidansa gwargwadon girmansa da darajarsa.

Sharadi na kyakyawan karatun wannan addu'a da kuma cewa dole ne a fara ta da yin sallah raka'a hudu (raka'a).[7]

Za a yi karatun (tilawa) na surar kadar a raka'a ta farko, suratu Zalzalah a ta biyu, surar kafirun a ta uku, da surori biyu na neman tsari (Suratul Falaq da suratu Al-) . Nas) a ta hudu.[8]

Bayan kammala karatun wannan addu'a, dole ne muridu ya kona turaren agarwood don sanya turare a dakin ko wurin karatun.[9]

  1. "Salatul Fatihi". www.tidjaniya.com. Archived from the original on 2021-04-19. Retrieved 2021-03-28.
  2. David, Robinson; Jean-Louis, TRIAUD (2005-01-01). La Tijâniyya: Une confrérie musulmane à la conquête de l'Afrique (in Faransanci). KARTHALA Editions. ISBN 978-2-8111-2224-9.
  3. Studia Missionalia: Vol. 21 (in Faransanci). Gregorian Biblical BookShop.
  4. Brenner, Louis (1984-01-01). West African Sufi: The Religious Heritage and Spiritual Search of Cerno Bokar Saalif Taal (in Turanci). University of California Press. ISBN 978-0-520-05008-2.
  5. Seesemann, Rüdiger (2011). The Divine Flood: Ibrahim Niasse and the Roots of a Twentieth-century Sufi Revival (in Turanci). Oxford University Press. ISBN 978-0-19-538432-1.
  6. Adnani, Jillali El (2007). La Tijâniyya, 1781-1881: les origines d'une confrérie religieuse au Maghreb (in Faransanci). Marsam Editions. ISBN 978-9954-21-084-0.
  7. "Salatul Fatih | Durood Fatih | Sholawat Fatih - Prayer of the Opener". Dua Hub (in Turanci). Retrieved 2021-03-28.[permanent dead link]
  8. Tijani, Saeed (2017-10-23). "SALATUL FATIH: The Importance of Salatul Fatih". SALATUL FATIH. Retrieved 2021-03-28.
  9. "Validity of Salat-ul-Fatih-Invoking Allah's Blessings upon the Prophet". Validity of Salat-ul-Fatih-Invoking Allah's Blessings upon the Prophet (in Turanci). Retrieved 2021-03-28.