Roman Oleksandrovych Bochkala ( Ukrainian : Роман Олександрович Бочкала, an haife shi a ranar 3 ga watan Mayun, 1984) ɗan jaridar Yukren ne, mai bada gudummawa, kuma wakilin soja. Dan jarida mai lamabar yabo a Ukraine (2013).[1] Wanda yayi aikin sa kai wa US Peace Corp a Ukraine. An ji masa rauni sosai a shekara ta 2014 kusa da Luhansk a lokacin farkon yakin Russo-Ukraine.[2] A lokacin rani na 2014, Bochkala ya sami nasarar gano shaidar sojojin Rasha da suke yaƙi da Sojojin Yukren a Gabashin Ukraine.[3]

Bochkala a cikin 2020
Roman Oleksandrovych Bochkala

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

Bochkaka ya fito ne daga Dzhankoi, Crimea, Ukraine. Ya shiga aikin jarida tun yana dan shekara 17. Da farko ya yi aiki a gidan jarida, sa'an nan a cikin tashar gidan telabijin na Ukraine ta 11 tashar, kuma daga baya a Chornomorsk TV tashar.

A shekara ta 2005, a cewar Bochkala, an kai masa hari, sakamakon haka an sa shi barci, an yi masa duka (ya damu karaya a wurare uku, idon sawu, gwiwa, kashin kafada, da hakarkarinsa) kuma an bar shi a some a dusar ƙanƙara. A lokacin, yana binciken gaskiyar kariyar da ’yan sandan masu safarar miyagun kwayoyi da wuraren tattara karafa suka yi.

A shekara ta 2007, ya shiga Interschool, sa'an nan a 2008 ya koma Kyiv kuma ya fara aiki a kan Inter TV tashar.

A matsayinsa na dan jarida, ya yi aiki akan rikicin soji da na cikin gida a Iran, Afganistan, Syria, Somalia, DR Congo, Kosovo, Lebanon, Rwanda, Liberia, Egypt, South Ossetia, Abkhazia, Jordan, Turkey.

Lambobin yabo

gyara sashe
  • Wanda ya lashe kyautar gasar 'yan jarida ta "Silver Feather" a shekara ta (2006)[4]
  • Lambar yabo na dan jarida na musamman a kasar Ukraine (2013)[5]
  • Kyautar Godiya ta Verkhovna Rada of Ukraine "Don ayyukan sadaukarwa a gankin fada da 'yan ta'adda" a shekara ta (2014)[6]
  • Teletriumph Award in the category "Reporter" (2015)[7]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://crimea.suspilne.media/ua/articles/56
  2. Gazeta.ua (2014-07-09). "Терористи біля Луганська поранили українського журналіста". Gazeta.ua (in Ukrainian). Retrieved 2022-10-18.
  3. Grytsenko, Oksana (2014-08-21). "Ukraine gets new evidence of Russian soldiers fighting on its turf (PHOTOS) - Aug. 21, 2014". Kyiv Post. Retrieved 2022-10-18.
  4. "Бочкала Роман Александрович". LB.ua. Retrieved 2022-10-18.
  5. "Роман Бочкала, Ігор Татарчук, Олександр Бондаренко та інші стали заслуженими журналістами (СПИСОК)". detector.media (in Harshen Yukuren). 2013-06-06. Retrieved 2022-10-18.
  6. "Медіаграмотність: практичні навички". courses.prometheus.org.ua (in Turanci). Retrieved 2022-10-18.
  7. MediaSapiens (2015-12-02). "Переможці «Телетріумфу»". ms.detector.media (in Harshen Yukuren). Retrieved 2022-10-18.