Rizi Timane, ɗan asalin Najeriya ne kuma a yanzu ɗan America, ya kasance mai nishadantarwa, kuma ƙwararren mai wayar da hankali kan bambancin jinsi wanda ke ba da kare haƙƙin masu canza jinsi wato "transgender". Shi ƙwararren likitan ilimin halayyar ɗan adam ne kuma mai lasisi tare da ƙwararrewa a fannin LGBTQIA.[1][2][3] Timane yana aiki a matsayin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya a cikin "Decker" akan Adult Swim Network, a matsayin baƙon tauraro a cikin shirin na lafiya na NBC; "New Amsterdam," da kuma labarinsa na canza jinsi (daga mace zuwa namiji) an nuna shi a cikin jerin shirye-shiryen Amazon Prime Documentary, "Outrageous".[1] Timane ya kafa cibiyar Happy Transgender Centeri a cikin shekarar 2012, kuma ya kafa gidauniyar Rizi Timane Annual Transgender Surgery Scholarship.[4]

Rizi Timane
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Tarayyar Amurka
Mazauni Los Angeles
Harshen uwa Turanci
Karatu
Makaranta Lagos,
Landan
University of Southern California (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a jarumi, psychotherapist (en) Fassara da mawaƙi
IMDb nm4548077
Rizi Timane

Kuruciya da Ilimi

gyara sashe

An haifi Timane a Najeriya ga dangin Kiristoci, kuma ya yi karatunsa na sakandare a makarantar kyauta na horar da sojoji da ke Jos, Jihar Filato.[1] Timane yana sha'awar transgender tun yana ƙarami (8yrs).[5] An kaishi shi zuwa Los Angeles don karatunsa bayan ya fuskanci jerin matsaloli a cikin muhallinsa da ake kyamar luwadi.[6] Ya yi karatun harkokin kasuwanci a London da Los Angeles kuma daga bisani ya zama Msc a aikin zamantakewa daga Jami'ar Kudancin California. Ya ci gaba da karatun addini, adalci na zamantakewa, da gwagwarmaya a makarantar Claremont School of Theology.

Timane ɗan wasan kwaikwayo ne, mawaƙi,[7] ƙwararren likitan ilimin haliyyar ɗan adam kuma ƙwararren likita ne na LGBTQIA.[8] Timane yanzu shine babban manajan Shirin Kiwon Lafiya na Transgender a St. John's Well Child da kuma Family Center a Los Angeles.[6]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 1.2 "Rizi Timane". IMDb. Retrieved 2022-06-18.
  2. "Dr. Rizi Nasele Bamaiyi Timane LCSW, DSW | Coach, Trainer, Entertainer | About &laquo". Retrieved 2022-06-18.
  3. "Consulting, Rizi Timane Psychotherapy and (2022-04-13). "Rizi Timane Psychotherapy & Consulting: Empowering the LGBTQ+ Community via Psychotherapy". GlobeNewswire News Room. Retrieved 2022-06-18.
  4. "Rizi Timane | HuffPost". www.huffpost.com. Retrieved 2022-06-18.
  5. Timane, Dr Rizi Xavier. "Spiritual Leader Dr. Rizi Timane Makes Plea for Human Rights Following Nigeria's Same Sex Marriage Prohibition Act". www.prnewswire.com. Retrieved 2022-06-18.
  6. 6.0 6.1 Fitzpatrick, Kyle (2018-06-26). "Rizi Timane Is Helping the Transgender Community, 1 Surgery at a Time". POPSUGAR News. Retrieved 2022-06-18.
  7. "Xavier Rizi Timane on Apple Music". Apple Music. Retrieved 2022-06-18.
  8. "Nigerian singer helps others with transgender surgery fund". NBC News. Retrieved 2022-06-18.