Razaq Adegbite
Razaq Akanni Adegbite (haife shi ne a ranar 20 ga watan Disamban shekarata 1992) a Nijeriya sana'ar sa ita ce kwallon kafa wanda a halin yanzu yake taka leda a matsayin dan wasan gaba na kungiyar gasannin firimiya ta kasar Hong Kong mai suna Happy Valley club.
Razaq Adegbite | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Lagos,, 20 Disamba 1992 (31 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka |
Kuruciya
gyara sasheTarihin Rayuwa
gyara sasheKaratu
gyara sasheHarkar Kwallo
gyara sasheAdegbite ya kuma fara wasan kwallon kafa ne da kungiyar matasa ta Karamone daga baya ya koma Gateway United, kafin daga baya ya koma Enugu Rangers . A cikin shekarar 2012 Enugu Rangers sun gargadi Enyimba Internstional, amma Adegbite ya yanke shawarar shiga Enyimba International, Jomo Cosmos (jinkirin izinin aiki) da kuma soke cinikayya da Kahramanspor saboda rashin jituwa game da batun canja wurin sannan aka dawo zuwa Najeriya domin kara kwantiraginsa da Enugu Rangers . Ya ci gaba da sanya hannu kan yarjejeniyar tare da Kano Pillars tsakanin 2016 da 2017. Ya shiga kulob din Doğan Türk Birliği na Cyprus a cikin 2017.
Wasanni a Matakin Duniya
gyara sasheRazaq ya samu damar buga wasanni 6, inda ya zira kwallaye 3 a ragar U-17 ta Nigeria . Rasaq ya kuma samu damar buga wasanni 7, inda ya zira kwallaye 4 a ragar U-20 ta Nigeria . A shekarar 2014, ƙungiyar ƙwallon ƙafan Najeriya ta kasa ta gayyace shi a wani wasan sada zumunci na kasa da kasa.
Gasar CAF na Camfiyon
gyara sasheYa taba buga wasa a ƙungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers International FC a gasar cin kofin zakarun Afirka ta CAF a shekarar 2012 zuwa 2013 da kuma Enyimba a shekarar 2013/14. An kuma canza shi zuwa Enyimba International FC lokacin da Enyimba ke matukar buƙatar sa kuma aka maye gurbinsa da Ifeanyi Ede zuwa Enugu Rangers .
Manazarta
gyara sashe
Hanyoyin haɗin waje
gyara sashe- Razaq Adegbite ya dawo - Savid News
- Razaq Adegbite at Soccerway