Enyimba International F.C.
Kungiya ce ta Kwallo a Najeriya
Enyimba International Football Club ko kawai ace Enyimba, takasance ƙungiyar wasan kwallon kafa ce a Nijeriya wanda ke a garin Aba, dake Jihar Abia, Nijeriya. Kungiyar dai na buga wasanni ne a Nigerian Professional Football League. Sunan kungiyar dai tana ma'anar Giwar al'ummah ne a Harshen Igbo kuma sunan ne akewa garin na Aba lakabi dashi. An samar da kungiyar a 1976, kungiyar tayi suna a shekarun 2000s kuma ana ganin kungiyar a mafi nasarar kungiyar acikin Nigerian football clubs, wanda ta lashe kofin African Champions League har sai biyu, da Nigerian championships guda shida (6) da kuma Federation Cup guda hudu (4) tun daga 2001.
Enyimba International F.C. | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | ƙungiyar ƙwallon ƙafa |
Ƙasa | Najeriya |
Mulki | |
Shugaba | Nwankwo Kanu |
Hedkwata | Aba |
Mamallaki | Jihar Abiya |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1976 |