Raphael Nomiye
Raphael Nomiye (Fabrairu 1963 - Nuwamba 2013) ɗan siyasar Najeriya ne kuma ɗan majalisa a majalisar wakilai ta Najeriya, mai wakiltar Ilaje dake Ese Odo na Tarayyar Jahar Ondo, Nigeria.[1][2]
Raphael Nomiye | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Ilaje, ga Faburairu, 1963 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mutuwa | Nuwamba, 2013 | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar jahar Benin | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Nigeria Labour Party |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Nomiye ne a ranar 6 ga watan Fabrairun 1963, a garin Ugbo, cikin ƙaramar hukumar Ilaje a jihar Ondo, a kudu maso yammacin Najeriya.[3] Ya halarci Kwalejin Kasuwancin Kings da ke Jihar Ribas da ke Kudancin Najeriya kafin ya samu digiri na farko a fannin harkokin gwamnati a Jami’ar Benin da ke Jihar Edo.[4]
Rayuwar Siyasa
gyara sasheA cikin shekarar 2011, jam'iyyar Labour ta Najeriya ta tsayar da shi takarar kujerar mazaɓarsa ta Ilaje da Ese Odo a Mazaɓar tarayya ta jihar Ondo, Najeriya,[5] wanda ya lashe zaɓen. Ya zauna a wannan kujera har zuwa rasuwarsa a cikin watan Nuwamban 2013.[6][7]
Duba kuma
gyara sashe- Zaɓen fidda gwani na Ilaje-Ese Odo
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://web.archive.org/web/20150402174034/http://www.tribune.com.ng/niger-delta/item/1102-ondo-bye-election-brothers-at-war/1102-ondo-bye-election-brothers-at-war
- ↑ https://web.archive.org/web/20150402125544/http://www.nigeriancurrent.com/ck88-news/raphael-nomiye-50-ondo-house-of-reps-lawmaker-slumps-dies
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2016-03-04. Retrieved 2023-03-18.
- ↑ https://saharareporters.com/2013/11/23/federal-rep-ondo-dies-apparent-heart-attack
- ↑ https://en.wikipedia.org/wiki/Raphael_Nomiye
- ↑ https://web.archive.org/web/20131130032149/http://www.thisdaylive.com/articles/nomiyes-death-stalls-onwuliri-oduahs-appearance-before-house-of-reps/165316/
- ↑ https://web.archive.org/web/20160305043221/http://m.nationalmirroronline.net/article/decision-day-in-ilaje-ese-odo-federal-constituency