Ranar dimokuradiyya ranar hutu ce ta ƙasa baki ɗaya a Najeriya domin tunawa da maido da mulkin dimokraɗiyya a shekarar 1999, wanda aka yi ranar 12 ga watan Yuni.[1] Har zuwa 2018,[2] ana yin bikin kowace shekara a ranar 29 ga Mayu.[3] Al'ada ce da ake gudanar da ita kowace shekara, tun daga shekara ta 2000. Ranar 12 ga watan Yuni aka fi sani da ranar Abiola, wanda aka yi bikin a Legas, Najeriya da wasu jihohin kudu maso yammacin Najeriya.[4][5]

Infotaula d'esdevenimentRanar Dimokradiyya
Iri public holiday (en) Fassara
Rana June 12 (en) Fassara
Ƙasa Najeriya

Tarihi gyara sashe

Wai-wa-ye gyara sashe

Najeriya ta samu ƴancin kai daga ƙasar Burtaniya a ranar 1 ga Oktoban 1960.[6][7] A mafi yawan tarihinta na 'yancin kai, Najeriya ta kasance ƙarƙashin wasu gwamnatocin sojoji, waɗanda suka shiga tsaka-tsakin lokaci na mulkin dimokradiyya (misali daga 1979 zuwa 1983 tare da Alhaji Shehu Shagari ). Babban shugaban mulkin soja na ƙarshe shine Janar Sani Abacha, wanda ya mutu kwatsam a shekarar 1998. Magajinsa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya yi alƙawarin miƙa mulki ga mulkin demokraɗiyya, don haka aka amince da sabon kundin tsarin mulki a ranar 5 ga Mayu, 1999. An gudanar da zaɓe kuma aka zaɓi Janar Olusegun Obasanjo mai ritaya, wanda a baya ya taɓa mulkin Najeriya a matsayin shugaban mulkin soja.

Ranar Dimokuradiyya gyara sashe

Tun da farko ranar 29 ga watan Mayu ita ce ranar dimokuraɗiyya a Najeriya, a daidai lokacin da sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya karɓi mulki a matsayin shugaban kasar Najeriya. A ranar 6 ga watan Yunin 2018, kwanaki takwas bayan 29 ga watan Mayu, 2018, aka yi bikin ranar dimokraɗiyya, gwamnatin tarayyar Najeriya ƙarƙashin jagorancin shugaba Buhari ta ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin sabuwar ranar dimokuradiyya ƙasar.[8] Anyi hakan ne domin tunawa da zaɓen dimokraɗiyya na MKO Abiola a ranar 12 ga watan Yuni 1993, wanda gwamnatin Ibrahim Babangida ta soke bisa kuskure. Daga baya an tsare MKO Abiola bayan da ya ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa a wancan lokacin.

Take gyara sashe

Attih Soul ne ya rubuta taken ranar dimokuradiyyar Najeriya bisa umarnin gwamnatin Buhari a shekarar 2017 a wani ɓangare na murnar zagayowar ranar.[9]

Duba kuma gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. Okogba, Emmanuel (2022-06-15). "2022 Democracy Day celebrations: Significant highlights from the president's speech". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2022-12-22.
  2. "Why I made June 12 Democracy Day -Buhari". Punch Newspapers (in Turanci). 2021-06-12. Retrieved 2022-12-22.
  3. Agbalajobi, Damilola. "June 12 is now Democracy Day in Nigeria. Why it matters". The Conversation (in Turanci). Retrieved 2022-12-22.
  4. "Letter to MKO Abiola on Democracy Day". TheCable (in Turanci). 2022-06-11. Retrieved 2022-08-01.
  5. Report, Agency (2019-06-11). "Democracy Day: Why June 12 is more significant than May 29 - Tinubu". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-12-22.
  6. Mohsin, Haroon (2022-07-08). "Nigeria Independence Day". National Today (in Turanci). Retrieved 2022-12-23.
  7. "How first coup still haunts Nigeria 50 years on" (in Turanci). 2016-01-15. Retrieved 2019-04-29.
  8. "Buhari declares June 12 Democracy Day, honours Abiola with GCFR". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2018-06-07.
  9. Unamka, Sampson (12 September 2020). "Attih Soul Shines Bright In RMF - The Nation" (in Turanci). Retrieved 2021-01-01.