Ramatu Yar'adua
Ramatu Yaradua kwamishiniya ce ta Hannun jari, Kasuwanci da Masana'antu na jihar Neja a Najeriya[1][2][3]
Ramatu Yar'adua | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Murtala Shehu Yar'adua (en) |
Karatu | |
Makaranta | Coventry University (en) Bachelor of Arts (en) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Rayuwa da Ilimi
gyara sasheRamatu ta taso ne daga wani ƙauye mai suna Enagi na ƙaramar hukumar Edati a jihar Neja.[4] Ta fara karatun firamari a Adrao International School, Lagos, daganan sai ta cigaba a ƙasar Birtaniya a makarantar Ibstock Place School London.[4] Ta karanta ilimin harkokin kasashen waje (International Relations) da kuma harshen Turanci a jami'ar Coventry University, inda ta gama da sakamakon matakin second class upper.
Aiki
gyara sasheRamatu ta fara aiki a matsayin mai kula da aiki a ma'aikatar kwantiragi da ake kira Platform Nigeria Limited, sananun ma'aikatar da ta kera gidajen haya na "Gwarimpa Estate", Abuja. Daga bisani an kara mata matsayi zuwa manajan kasuwanci (Marketing Manager), inda take kula da tasirin ayyuka da sakamako na gari na kamfanin. Bayan ta ajiye aiki da kamfanin Platfrom Limited, Rahmatu ta fara aiki da kamfanin MicroAccess Limited, daya daga cikin wadanda suka fara samar da ayyukan bayanai da sadarwa a Najeriya, a matsayin babbar mai kula da harkokin kasuwanci. A yayin da take aiki a wannan kamfanin, ita ke kula da wasu manya manya ayyukan kamfanin kamar su Babban Asibitin Najeriya dake Abuja, Ma'aikatar Corporate Affairs Commission da kuma Tarayyar Najeriya.
Har wayau, Ramatu tayi aiki a matsayin darakta a ma'akatar Hamble Group ta kasar Burtaniya, sannan a yayin da ta dawo gida nahiyar Afurka, Ramatu ta cigaba da rike matsayin Darakta na Hamble Group (Afurka).
Siyasa
gyara sasheTa kasance tsohuwar kwamishiniyar kasuwanci da masana'antu da bada jari na jihar Neja. [5]
Rayuwar ta
gyara sasheTa auri Alh Murtala Shehu Yar’adua, tsohon ministan tsaro na Najeriya.[6]
Mahaɗun waje
gyara sashe- https://minvestment.nigerstate.gov.ng Archived 2020-11-27 at the Wayback Machine
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.von.gov.ng/twenty-commissioners-join-niger-state-executive-council/. Missing or empty
|title=
(help)[permanent dead link] - ↑ NewNigerianNewsPapers (2019-10-31). "Twenty Commissioners Take Oath Of Office In Niger, None Allocated Information Portfolio". New Nigerian Newspaper (in Turanci). Archived from the original on 2020-11-27. Retrieved 2020-11-19.
- ↑ NewNigerianNewsPapers (2019-10-31). "Twenty Commissioners Take Oath Of Office In Niger, None Allocated Information Portfolio". New Nigerian Newspaper (in Turanci). Archived from the original on 2020-11-27. Retrieved 2020-11-19.
- ↑ 4.0 4.1 "A Brief Biography Of Rahmatu Yar'adua, Current Commissioner And HOR Aspirant". IbabaNaija (in Turanci). 2018-09-16. Archived from the original on 2020-11-27. Retrieved 2020-11-19.
- ↑ "My Root: My Pride and Source of Inspiration---Hajiya Yar'adua". Nigerian Voice. Retrieved 2020-11-19.
- ↑ "A BREIF ON HAJIYA RAHMATU MOHAMMED YAR'ADUA, NIGER STATE COMMISSIONER FOR INVESTMENT, COMMERCE AND INDUSTRY – Faces International Magazine" (in Turanci). Archived from the original on 2020-11-27. Retrieved 2020-11-19.